Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayana Dalilan yin Gwanjon motocin ta na aiki da suka tsufa. Mai magana da yawun hukumar a nan Kano Sadiq Muhammad Maigatari,ne ya bayana hakan a zantawarsa da manema labarai. Muhammad Maigatari, ya Kara da cewa, “mafi yawacin motocin da hukumar ke aiki da su dama Wanda suke tsaye a ofisoshin hukumar sun tsufa tare da wuce shekarun da ya kamata a ce suna aiki da su bisa doka” Mai magana da yawun hukumar NDLEA a nan Kano Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma ce,”cigaba da aiki da tsafin motocin…
Author: Wafsym
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bingida mai suna Gwaska a jihar Katsina tare da wasu 100 a wani harin da sojojin suka ƙaddamar kan masu aikata miyagun laifuka a jihar da ke arewa masu yammacin kasar. Kwamishinan Tsaro da Lamuran Cikin Gida na Jihar, Dr. Nasir Mua’zu, ne ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. Ya ce aikin na soji wani muhimmin ɓangare ne na dabaru da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ke bi wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Katsina da Arewa Maso Yammacin ƙasar. A lokacin harin, dakarun sun ƙwato tare…
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Mai Alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad III, ne ya bayyana haka a yau Asabar a Sakkwato. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadan nan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya. Muna yiwa dimbin musulmin duniya barka da sallah.
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Kano ta aike da jami’ai 1,889 domin gudanar da aiki na musamman a lokacin bukukuwan karamar sallah da nufin tabbatar da ingantacciyar zirga-zirga da kare lafiyar matafiya a manyan hanyoyi. Kwamandan hukumar a Kano, Ibrahim Abdullahi Matazu, ya bayyana cewa wannan shiri zai gudana daga ranar 27 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, tare da hadin gwiwar jami’ai 1,348 na dindindin da 541 na musamman. Jami’an za su kula da zirga-zirga, aiwatar da dokokin hanya, da kuma bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka tsinci kansu a hatsari. Matazu ya bukaci direbobi su…
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata gudanar da bincike bayan gano wani guri da take zargin ana yin aikin tashar saukar jirgin sama ba bisa kaida ba tare da rufe hanyar da manoma ke zuwa gonakinsu a garin Tiga dake karamar hukumar Bebeji. Sakataren kwamitin gwamnatin Kano dake yaki da gine-gine ba bisa kaida ba Hamid Sidi Ali, shi ne ya bayana hakan ga manema labarai lokacin da kwamitin ya ziyarci gurin da ake aikin da safiyar ranar Jumma’a. Wasu cikin masu gonaki a yankin sun bayana cewa tun lokacin da aka fara aikin da suke zaton tashar jirgin sama…
Wasu ‘yanfashin daji sun kashe dakarun rundunar tsaron jihar Zamfara 10 a wani kwanton ɓauna da suka yi musu ranar Asabar. Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ce shida daga ciki dakarun tsaron gwamnatin jihar ne da ake kira Askarawa, huɗu kuma ‘yan sa-kai ne. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya ƙara da cewa akwai dakarun Asakarawa biyu da ɗan sa-kai ɗaya da suka ɓata. “Lamarin ya faru ne bayan farmakin da gamayyar jami’an tsaro [ciki har da Askarawa] ƙarƙashin jagorancin sojojin Najeriya suka kai wa sansanin ‘yanbindiga a Dajin Sunƙe, wanda aka samu gagarumar…
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana takaicinsa kan rahotannin da suka nuna ana rage albashin wasu ma’aikatan gwamnati ko kuma hana su albashinsu gaba ɗaya, yana mai cewa hakan babban cin zarafi ne ga haƙƙin ma’aikata kuma cin amanar jama’a. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis. Gwamna Yusuf, wanda ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan labarin cewa wasu ma’aikata sun kwashe watanni ba tare da an biya su haƙƙinsu ba, ya yi alkawarin binciko masu hannu a wannan aika-aika tare da…
El Rufai ya ce kamawa da tsarewa harma da kuma azabtar da abokan adawar siyasa ba wani sabon abu ba ne a rayuwa, saboda an taɓa tsare shi har sau 3 a baya sakamakon bayyana ra’ayoyinsa akan gwamnatocin da suka gabata. Saboda haka, tsohon gwamnan ya ce kame da azabtarwar ba wani sabon abu bane, kuma Allah kadai ke sanyawa Bil Adama lokacin barin duniya. El Rufai ya shaidawa mutanen da ya ce basa bacci duk lokacin da yake Nijeriya da su ƙwan da sanin cewar yana kan hanyar komawa kasar domin halartar bikin ƙaddamar da littafin tsohon shugaban ƙasa…
Gwamnatin sojin ƙasar Niger ta tabbatar da cewa wani harin kwantar ɓauna da ‘yan ta’adda suka kai ya yi sanadin mutuwar sojojinta guda goma a kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso. A wata sanarwa da gwamnatin sojin ƙasar ta karanto a ranar Laraba da dare, ta bayyana cewa an tura jami’ai zuwa yammacin ƙasar a ranar Litinin domin kama ɓarayin shanu a ƙauyen Takzat. “A lokacin wannan aikin ne wani gungun masu laifi ya yi wa jami’an tsaron kwanton-ɓauna wanda hakan ya kai ga rasa sojojinmu goma,” in ji sanarwar. Duk da cewa maharan sun yi ƙoƙarin guduwa amma…
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Darakta janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), a kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an sace tsohon Shugaban NYSC din ne da karfe 12:30 na safiyar ranar Alhamis inda wasu mahara dauke da muggan makamai suka afkawa al’ummar garin, inda suka rika harbe-harbe a kai a kai domin sanya fargaba da tsoro a tsakanin mazauna yankin. Daga bisani ne sukayi awan gaba dashi. Har ya zuwa lokacin bayar da wannan rahoton hukumomi ba…
