Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Sojojin Nijeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da wasu ‘yan bindiga 100 a Katsina
Afrika

Sojojin Nijeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da wasu ‘yan bindiga 100 a Katsina

April 12, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bingida mai suna Gwaska a jihar Katsina tare da wasu 100 a wani harin da sojojin suka ƙaddamar kan masu aikata miyagun laifuka a jihar da ke arewa masu yammacin kasar.

Kwamishinan Tsaro da Lamuran Cikin Gida na Jihar, Dr. Nasir Mua’zu, ne ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce aikin na soji wani muhimmin ɓangare ne na dabaru da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ke bi wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Katsina da Arewa Maso Yammacin ƙasar.

A lokacin harin, dakarun sun ƙwato tare da lalata bindigogi masu jigida biyu da bindigogi da aka ƙera a gida biyu da sauran makamai domin hana masu aikata miyagun laifuka sake amfani da su.

Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin Nijeriya tare da ɓangaren sojin saman ƙasar ne suka ƙaddamar da hare-haren ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025 a dabar ɓarayin daji a Mununu Bakai da Zango da Jeka Arera da Malali, da kuma Ruwan Godiya duka a cikin ƙananan hukumomin Kankara da Faskari.

“Hare-haren da suka yi daidai kan ɓarayin, bisa bayanan sirrin da aka samu, sun yi silar kashe wani wanda ake nema ruwa-a-jallo da aka fi sani da Gwaska, wanda mataimaki ne ga wani shugaban ‘yan bindiga mai alaƙa da ISWAP,” in ji shi.

“A iya cewa wannan aikin ya yi nasarar katse ayyukan masu aikata miyagun laifukan da suka daɗe suna aikata ta’addanci a ƙauyuka da garuruwa da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur LGAs,” in ji shi.

Kazalika, dakarun tsaro sun ƙaddamar da wani aiki da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025, a hanyar da ɓarayin daji ke bi a Dutsen Wori gefen hanyar  Dandume zuwa Kandamba, da ke wajen garin Dandume a kan iyaka da ƙananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

El-Rufa’i ya sake zargin yunƙurin kama shi

April 21, 2026

Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

April 20, 2026

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.