Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kone tan 12.2 na miyagun ƙwayoyi da haramtattun magunguna da ta ƙwace daga hannun masu safara a Jihar Kano, yayin da ta bayyana cewa ta kama mutum 904 bisa laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi tsakanin watan Janairu da Yunin 2026.
An gudanar da aikin kone ƙwayoyin ne a ranar Litinin a Kano, inda Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Ibrahim Faroukh, ya wakilta, ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yaƙi da shaye-shaye da duk wani nau’in laifi.
Faroukh ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na ci gaba da zama babbar barazana ga zaman lafiya, tsaro da makomar matasa, yana mai cewa gwamnatin Kano ba za ta bari masu aikata laifuka su lalata rayuwar al’umma ba.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tura jami’an tsaro sama da 1,000 zuwa wurare 52 da aka gano a matsayin maɓoyar masu aikata laifuka, lamarin da ya kai ga kama mutane da dama tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi masu yawa.
A cewarsa, gwamnatin ta kuma ƙaddamar da shirin Kano Safe Corridor Initiative, domin ba da shawara, gyaran hali, horas da sana’o’i da sake dawo da masu fama da shaye-shaye cikin rayuwar al’umma.
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bai wa NDLEA motocin aiki guda uku domin ƙarfafa ayyukanta, tare da alƙawarin ci gaba da mara wa hukumomin tsaro baya.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NDLEA ta ƙasa, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), wanda aka wakilta, ya ce kone miyagun ƙwayoyin wata alama ce da ke nuna cewa doka ta yi aiki, yana mai cewa duk kilogram ɗaya da aka lalata na nufin an kare rayuka da kuma al’umma daga illar shaye-shaye.
Ya kuma yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta yi sassauci ga masu safarar miyagun ƙwayoyi ba, tare da nuna damuwa kan yadda ake karkatar da magungunan da doka ta kayyade, musamman Tramadol, Codeine da Pentazocine, zuwa kasuwar baƙi.
Marwa ya ce hukumar ta kafa kwamitocin haɗin gwiwa da Ƙungiyar Masana Magunguna ta Najeriya (PSN), domin ƙarfafa sa ido kan rarraba irin waɗannan magunguna da kuma inganta musayar bayanan sirri.
Ya kuma buƙaci manyan makarantu da jami’o’in Kano su rungumi shirin gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi na NDLEA domin kare ɗalibai daga shiga harkar shaye-shaye.
Tun da farko, Kwamandan NDLEA na Kano Strategic Command, CN Dahiru Yahaya Lawal, ya ce an kone kilogram 12,233.946 na miyagun ƙwayoyi da haramtattun magunguna, inda kilogram 11,890.427 aka ƙwace a faɗin Kano, yayin da kilogram 343.519 aka kama a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
Ya ce daga watan Janairu zuwa Yunin 2026, rundunar ta kama mutum 904, waɗanda suka haɗa da maza 869 da mata 35, tare da ƙwace fiye da tan 2.5 na miyagun ƙwayoyi.
Lawal ya ƙara da cewa kotuna sun yanke wa mutum 54 hukunci kan laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, inda wasu suka samu zaman gidan yari har na tsawon shekaru 15.
Ya bayyana cewa hukumar ta kuma tarwatsa wasu manyan hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi ta hanyar gudanar da Operation Sharar Mafaka da Operation Ramadan Mubarak, waɗanda suka kai ga gano ramuka da kogunan da masu safara ke amfani da su wajen ɓoye miyagun ƙwayoyi a yankin Rimin Kebe.
Sai dai ya jaddada cewa yaƙi da shaye-shaye ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, yana mai kira ga sarakunan gargajiya, malamai, iyaye, makarantu da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai da NDLEA domin daƙile yawaitar shaye-shaye da kuma tallafa wa masu son gyaran hali.

