Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Fagen Wasannin DNN Hausa
Wasanni

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
arder2
arder2

Jamal Musiala ya dawo kuma zai bi tawagar Bayern zuwa Spain a wasan da zasu fafata da Barcelona ranar Laraba.

Jaridar AS ta rawaito Joan Laporta bai manta da dokewar da Bayern ta yi musu da ci (8-2) ba, lokacin da Flick yake horas da ƙungiyar ta Germany kuma Laporte ya nemi da ya rama hakan a wasa na gaba.

Flick ya mayar masa da martanin cewa ko da basu rama 8 ba idan suka samu nasara ya wadatar.

Yanzu haka Ƙungiyar Vincent Kompany ta buga wasanni 10, inda ta zura ƙwallaye 37 ya yin da aka zura mata ƙwallaye 10 akan ƙiyasin ƙwallo ɗaya a kowanne wasa.

Ƙungiyar Hansi-Dieter Flick ta buga wasanni 12, inda ta zura ƙwallaye 39 ya yin da aka zura mata ƙwallaye 12 akan ƙiyasin ƙwallo ɗaya a kowanne wasa.

Waɗannan lambobi na nuna cewa zamu shedi wasa mai cike da ƙalubale ga ƙungiyoyin biyu kuma wasa mai zafin gaske wanda kowannen su yana da kyau ta ɓangaren baya da kuma gaba.

MARCA ta rawaito cewa Bayern Munich ita ce ƙungiyar da Dani Olmo ya fi jin daɗin fafatawa da ita a sana’ar sa ta ƙwallon ƙafa, inda ya zura musu ƙwallaye huɗu a haɗuwar da sukai, ciki har da ƙwallaye uku rigis da ya ci su a gasar German Super Cup 2023.

A Hukumance an sanar da alƙalin wasa Anthony Tailor a matsayin wanda zai busa wasan Arsenal da Liverpool ranar Lahadi, Michael Salisbury zai kula da na’urar VAR.

Karo na farko a tarihin gasar Premier League ɗin Ingila, ƙungiyoyi huɗu sun gaza samun nasara ko ɗaya bayan zagaye na 8 a gasar.

Ipswich Town
Crystal Palace
Wolves
Southampton

 

RAC1 ta rahoto | Bawai iya rashin lafiya ba ce ta sa De Jong bai buga wasan Sevilla ba, ɗan wasan ya yi wani abu wanda ya ɓata wa Flick rai.

Ba lallai ne ya kasance matsalar ladabtarwa ba ce amma dai wani abu ya faru da Frenkie wanda kuma bai yiwa mai horaswar daɗi ba.

Flick ya tura masa saƙo shekaran jiya na sanya shi motsa jiki tun bayan dawowa hutun rabin lokaci batare da ya sanya shi a cikin wasan ba har aka tashi.

Antonio Conte: “Yana da kyau a gare ni na lashe Italian Cup domin Napoli. Wannan shine aiki na kuma shine abun da yakamata na yi…Bawai iya karawa ba. Harma da nasara.”

Joshua Zirkzee yana a buɗe domin ya komaa Italiya, mai yiwuwa nan da watan Janairu.

Babu tabbas ko Manchester United za ta yi la’akari da komawarsa a matsayin aro, amma Juventus ta nuna sha’awarta kan dan kasar Holland din.

Juventus ta ce an yi mata ƙutse cikin ɗaya daga shafukanta ya sada zumunta a jiya Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan magoya bayanta sun fara murna kan bayanin da aka wallafa na ƙarya, na cewa za ta sayi ɗan wasan Real Madrid ɗan ƙasar Turkiyya Arda Guler.

Duk da cewa kasuwar musayar ‘yan wasa a Turai rufe take, amma labarin ya rikita magoya bayan Juventus, saboda hoton ɗan wasan da aka sa a X, rike da jaka a filin jirgin sama ya nufi Italiya.

A saman a rubuta barka da zuwa Juventus Arda Guler.

Juventus ta ce magoya bayanta su yi watsi da labarin wanda ta ce na ƙanzon kurege ne.

Daraktan Juventus Giuntoli ya tabbatar da cewa an kammala yin aiki tsakanin Paul Pogba da kungiyar.

“Pogba babban dan wasa ne amma muna kan wasu tsare-tsare daban-daban yanzu”.

Pogba ya bar Juve a matsayin dan wasa na kyauta.

Bayer Leverkusen na shirye-shiryen tafiyar kocinta Xabi Alonso a bazara mai zuwa, Inda tsohon dan wasan Sifaniyan ke jan hankalin Real Madrid da Manchester City, idan Pep Guardiola ya tafi. (Sky Germany)

La Liga na neman izinin hukumar kwallon kafa ta Sifaniya da Uefa da kuma Fifa domin gudanar da wasan da Barcelona za ta yi da Atletico Madrid a watan Disamba a birnin Miami. (Mail)

Arsenal na shirin zawarcin Brentford dan kasar Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, sakamakon tagomashin da ya ke samu a farkon kakar wasa ta bana. (Football Insider)

Arsenal na nazarin hanyoyin kara girman filin wasan Emirates. (Times)

Julen Lopetegui ba ya fuskantar sallama a matsayinsa na kocin West Ham duk da rashin fara kkakr wasan bana da ƙafar dama da kungiyar ta yi. (Guardian)

Arsenal da Chelsea na sa ido kan dan wasan Juventus ɗan ƙasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 24.

Toni Kroos ya ce: “Abu mafi wahala shine faɗawa Ancelotti da kuma Ɗana cewa zan yi ritaya daga buga kwallon kafa.”

Nasser El Khelaifi ya ce “Lokacin da Messi ya zo Paris, ban yi tsammanin zamu samu babbar riba mai yawa kamar yadda muka samu ba. Sai da ta kai ga mun kulle shagon siyar da kayayyakin mu na kwanaki biyu saboda neman abubuwan da ake ya wuce ƙa’idar yadda muka tana da kuma rigunan da ke shagon sun ƙare da wuri.

Kowa burinsa ya sai rigar Messi. Kai ko shafin mu na yanar gizo sai da ya yi ƙasa saboda yawan mutanen da ke bibiyar sa. Shafukan mu na sada zumunta sun ƙara yawan mabiya cikin ƙanƙanin lokaci, amma hakan dai dai ne akan ɗan wasa mafi kyau a duniya.

Abun da yafi burge ni sosai shine ban taɓa ganin Messi ya damu akan kuɗi ba kuma baya magana akan kuɗi gaba ɗaya. Kawai yana son jin daɗin sa da na ƴaƴan sa. Na yi ƙoƙari wajen ganin na tsawaita zaman sa a PSG da albashi mai tsoka, amma ya faɗa min zai tafi ya fara wani sabon aikin. Girmamawa ce a gare ni da na sanya kwantaragi da gwarzon ɗan wasa a tarihin ƙwallon ƙafa kuma Paris ko da yaushe tana maraba da shi a duk lokacin da ya so.” (Al Sharjah).

Hukumomin La Liga na son a buga wasan Barcelona da Atletico Madrid da aka tsara yi a watan Disamba a birnin Miami – amma idan Fifa ta amince.

Wannan zai zama karon farko da za a buga wasan La Liga a Amurka.

Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa ce za ta yanke hukunci na ƙarshe kan wannan buƙata.

An tsara buga wasan ne a ranar 22 ga watan Disamba, gabanin La Liga su ta fi hutun lokacin sanyi.

Daga Barcelona har Atletico na cikin ƙungiyoyi huɗu da aka tsara za su buga Super Cup na Spain a farkon watan Janairu, wanda ake buga a Saudiyya.

A watan Afrilu ne Fifa ta fice daga kalubalantar da aka yi mata da Relevent ya jagoranta, wanda ya nemi ta rika sanya idanu kan wasannin da ake yi a Amurka.

Watan da ya biyo baya Fifa ta sanar da kafa wani kwamiti da zai duba yadda za a riƙa haɗa wasanni a ƙasashen waje.

Shugaban gasar La Liga Javier Tebas ya bayyana buƙatarsa ta a riƙa ɗaukar wasannin La Liga zuwa wasu ƙasashen.

Barcelona ta so buga wasa da Girona a Miami a watan Janairun 2019, sai dai buƙatar ta fuskanci suka daga wasu a hukumar kwallon kafa ta La Liga da kuma ƙungiyar tsofaffin ‘yan wasan Barcelona.

Wasu majiyoyi daga La Liga sun ce har yanzu akwai sauran aiki amma suna da kwarin gwiwar za su samu amincewar Fifa kan hakan.

Manchester United na shirin sauraron tayin aro kan ɗan wasan Brazil Antony, mai shekara 24 a watan Junairu. (Insider Kwallon Kafa)

Tsohon dan wasan Italiya da Roma Francesco Totti, mai shekara 48, ya ce wataƙila ya koma taka leda bayan ƙungiyoyin Seria A sun tuntube shi. (Gazzetta Dello Sport)

Arsenal da Aston Villa da Newcastle na zawarcin ɗan wasan Red Bull Salzburg mai shekara 20, Oscar Gloukh. (Caught Offside

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024

FA ta dakatar da Mudryk daga buga kwallo – Barcelona ta dauki dan kasar Mali Ibrahim Diarra (17) daga Academia África Foot – FAGEN WASANNI

December 17, 2024

Waye gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afrika na 2024?

December 16, 2024

FAGEN WASANNI – Real Madrid ta kara kaimi wajen zawarcin Alexander-Arnold daga Liverpool

October 9, 2024

Jude Bellingham zaiyi jinyar makwanni

August 23, 2024
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Kano

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

By WafsymApril 13, 2025

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayana Dalilan yin Gwanjon…

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

January 20, 2025

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.