Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano
Nishadi

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

January 20, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
WhatsApp Image 2025 01 20 at 13.32.29

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan korafe-korafen da al’umma suka shigar gabanta tare da wasu malamai a Jahar Kano kan Usaman Sojaboy dangane da wani sabon salon waka da yake kokarin fitowa da shi a wanda ya saba da koyarwar addinin musulunci tare da al’adar malam Bahaushe.

A wata sanarwa da jami’in yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya aminche da kwace lasisin mawakin Sojaboy da Shamsiyya Muhammad tare da Hassana Suzan ya yin da sanarwa ta bukaci masu gidajen wasanni tare duk wani wannda yake mu’amalar aiki dasu da ya yi biyayya ga wannan matakin na Hukumar domin cigaban Jahar Kano.

Abba El-mustapha ya baiwa sashin tace fina-finai na Hukumar umarnin cewa daga wannan lokacin kada a Kara tace duk wani film da aka hangi fuskokinsu a ciki tare da kira ga masu shirya fina-finai musamman daraktoci da su kiyayi yin duk wata huldar aiki dasu domin gujewa fishin Hukumar.

Kafin ta dauki irin wannan matakin Hukumar na yin iya kokarinta kan gargadar masu irin wannan halayya nasu kiyayi yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko Sana’arsu inda ta Kara jaddada cewa buzata dauki duk wani abu da zai taba addini, al’ada ko tarbiyar a’lummar Jahar Kano da sauki ba. Haka kuma, bazata goyi bayan ire-iren wannan halayyar ba da sunan sana’a a Jahar Kano.

Idan ba’a manta ba a watan da ya gabata ne Hukumar ta dauki irin wannan mataki ga daya daga cikin fitattun jarumai a Masana’antar ta kannywood wato Samha M Inuwa da nufin tsaftace Masana’antar tare da tabbatar da kowa nabin dokokin Hukumar sau da kafa.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamnan Kano ya naɗa Sani Danja mai ba shi shawara na musamman

December 15, 2024

Yau ta ke ranar masoya Shayi ta duniya – 15 December.

December 15, 2024
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Kano

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

By WafsymApril 13, 2025

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayana Dalilan yin Gwanjon…

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

January 20, 2025

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.