A yau ne 15 ga watan Disamba, kuma masoya shayi a faɗin duniya ke bikin ranar shayi ta duniya.
A nan Kano, wasu masu sha da sana’ar shayi na gudanar da bikin ranar cikin farin ciki, inda masu sayar da shayi da masu ta’ammala da shi suka taru domin karrama wannan abin sha da zukata ke matuƙar so.
Ranar shayi ta duniya, wadda majalisar ɗinkin Duniya ta samar a shekarar 2019, ana bikin murnar ranar ne a matsayin wata al’ada kuma abun bun ƙasa tattalin arziƙi.
A birnin Kano, wasu masu sana’ar shayi sun ce su na sane da bikin wannan rana kuma suna gudanawa duk shekara, wasu kuma basu san da ita ba.
Akwai wasu masu ta’ammali da shayi da suka ce, “shayi ya kasance jigon rayuwar mu ta yau da kullum, ko a gurin shagulgulan biki ko gurin aiki shi ne ke ƙara masa armashi”.
Shayi na da matuƙar tasiri a rayuwar Malam Bahaushe, kasan cewar hausawa na cikin al’ummomin da suka cuɗanya sosai da sauran ƙabilu masu ta’ammali da shayi a rayuwar yau da gobe, domin ko a yanayi na sanyi ko zafi ko damuna alamura basa tafiya yadda ya kamata batare da ƙurbar shayin ba.
Baƙin shayi wanda ake kira da ruwan bunu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan dake kama ɗan Adam, wanda idan ba’a samu ba ya kan zama wata damuwa ko cikas a rayuwar mai shanshi.
Malam Rumfar kara wani tsohon mai sayar da shayi ne a unguwar Kurna dake Kano, ya bayyana ra’ayinsa kan bikin wannan rana.
“Idris Army Journalist, mashayin shayi ne kuma ɗan Jarida a Kano, ya ce “shayi wani ɓangare ne na asalinmu ƴan Kano, domin yana haɗa jama’a guri guda, walau a gurin aiki, ko lokacin tattaunawar kasuwanci ko kuma taron dangi, hasalima ba iya abin sha ba ne kawai; al’ada ce”.
Hajiya Maryam Abdullahi Wangara, ƙwararriya ce kan harkokin noma, kuma mataimakiyar shugaban ƙungiyar Manoma ta gida gida famers association dake Kano, ta jaddada bukatar gwamnati ta saka hannun jari a harkar noman kayan shayi.
“Akwai gayayyaki da a yanzu ake sakawa a shayi, a shekarun baya bumu sani ba, zaifi kyau kuma ace anan Arewa ake nomansu domin zai bun ƙasa tattalin arziƙin mu”. Inji Maryam
Wasu mazauna birnin Kano sun yi tsokaci kan muhimmancin shayin ba wai kawai a matsayin abin sha ba, harma da sanya yasu farin ciki da annashuwa.
Godiya da jinjina ga irin rawar da shayi ke takawa a rayuwarmu ta yau da kullum