Shugaban Karamar Hukumar Dala Ya Yi Kira Ga Masu Hannu Da Shuni Su Tallafawa Yunkurin Gwamnati Don Bunkasa Ilimi Da Lafiya
Shugaban karamar hukumar Dala, Alhaji Surajo Ibrahim Imam, ya yi kira ga masu hannu da shuni da kamfanoni su tallafawa yunkurin gwamnati na bunkasa ilimi da lafiyar al’umma. Ya bayyana hakan ne yayin bikin bude dakunan gwajin kimiyya (laboratories) a makarantar mata ta GGC Dala, wanda aka gudanar tare da halartar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi II.
Dakunan gwajin da aka kaddamar sun hada da:
Chemistry Laboratory mai suna Gwamna Eng. Abba Kabir Yusuf,
Physics Laboratory mai suna Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi,
Biology Laboratory mai suna A.B. Mahmud SAN,
Agricultural Laboratory mai suna Alhaji Umar Haruna Doguwa.
Wannan aiki ya samu tallafi daga wani babban kamfanin sadarwa wanda ya dauki nauyin samar da wadannan dakunan zamani. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Surajo Imam, ya yaba wa kokarin kamfanin, tare da godewa hamshakin attajirin nan, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya bayar da gudummawar kudi da aka yi amfani da su wajen sayen kayan aiki na asibitoci domin bunkasa kiwon lafiyar al’umma.
A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi II, ya bayyana jin dadinsa bisa wannan ci gaba, yana mai bayyana makarantar GGC Dala a matsayin makaranta mai tarihi wacce aka kafa tun shekaru 64 da suka wuce. Sarkin ya kuma yabawa kokarin daliban makarantar wajen karatun Alkur’ani mai tsarki, tare da kira ga kamfanoni su ci gaba da tallafawa bangaren ilimin kimiyya a Najeriya.
Wakilin kwamishinan ilimi na jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, wanda sakataren ma’aikatar ilimi ya wakilta, ya yaba wa wannan kokari, tare da godewa Sarkin Kano da kamfanin sadarwa bisa wannan gudunmawa.
Shugaban makarantar GGC Dala, Hajiya Ramatu Muktar Tofa, ta jinjina wa wadanda ke tallafawa makarantar, ciki har da Alhaji Aminu Dantata, kungiyar tsofaffin daliban makarantar karkashin Hajiya Saudatu Sani, da kuma kungiyar iyaye da malamai karkashin Alhaji Ado Muktar Adnan. Ta kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na farfado da harkar ilimi a jihar Musamman
Taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da Hakimai, shugabannin unguwanni, shugaban jam’iyyar NNPP na Dala, kansiloli, da masu ba da shawara ga shugaban karamar hukumar.