Wata Dorinar ruwa ta hallaka mai gadin wani gidan gona da ake kira gidan gonar Orchard, mallakin Sarkin Yauri, Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi.
Mai gadin maisuna Malam Usman Maigadi, ya rasa rashi ne lokacin da ya shiga kogin Yauri dake kauyen Tillo a jihar Kebbi yana kamun kifi.
Rahotanni sunce dorinar ruwan ta farmaki mai gadin mai kimanin shekaru 60 a duniya lokacin da tayi zaton yaje ne zai ɗaukar mata ɗanta, saboda haka itama saita afka masa a wani salo na kare kai daga daukar mara da ko dauka.
Shugaban karamar hukumar Yauri, Alhaji Abubakar Shu’aibu ya tabbatar da cewa an yi jana’izar marigayi Maigadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Bayan sallar jana’izar da aka gudanar a garin Yauri, Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya jajantawa masarautar Yauri da iyalan mamacin.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Alhaji Ahmed Idris ya fitar, gwamnan ya bukaci ‘yan uwa da masarauta da su amince da ƙaddara.
Ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.