Allah Ya yi wa Alhaji Sani Gwarzo, wanda aka fi sani da “Tumbuleke”, rasuwa.
Alhaji Sani Gwarzo ya rasu ne a yau Talata, a Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, bayan fama da rashin lafiya.
Labarin rasuwar marigayin ya jefa ’yan uwa, abokan rziki da sauran masoyansa cikin jimami da alhini.
Alhaji Sani Gwarzo ya kasance mutum da mutane da dama suka san shi, kuma rasuwarsa ta haifar da babban gibi ga iyalansa da wadanda suka san shi.
A wannan lokaci na alhini, muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, ’yan uwa da abokan arziki.
Muna rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya ba iyalansa da sauran wadanda suka yi rashi hakurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya gafarta maka, Alhaji Sani Gwarzo “Tumbuleke”. Allah Ya sa Aljanna ce makomarka. Amin.

