Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ingila ta dakatar da ɗan wasan Chelsea Mykhailo Mudryk daga buga wasa zuwa wani ɗan lokaci, bisa zarginsa da ta’ammali da ƙwayoyi.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta tabbatar da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ingila ta tuntuɓeta akan dan wasanta Mykhailo Mudryk game da zargin da ake yi masa na yin amfani da ƙwayoyi ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ta Gano Hakan ne bayan gwajin fitsari da aka yi masa tare da wasu ƴan wasa.
“Dukkan kungiyar mu har da Mykhailo Mudryk muna ba da cikakken goyon baya ga hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) akan gwajin da take yi akai-akai, har da Mykhailo Mudryk.
“Mykhailo ya tabbatar da cewa bai taɓa amfani da wasu haramtattun kwayoyi da gangan ba.
A halin yanzu, Mykhailo tare da mu zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin da abun ya shafa domin gano bakin zaren al’amarin da ya haifar da wannan sakamakon. Ba zamu kara tsokaci akai ba.” Inji Chelsea
Kungiyoyin Bayern Munich da Real Madrid da Manchester City sun cire rai a farautar ɗan wasan Jamus mai shekara 21, Florian Wirtz, bayan Bayer Leverkusen ta shirya tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2028.
Manchester United ta sa ɗan wasanta na Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27 a kasuwa kuma za ta amince da zabtare farashinsa a watan Janairu.
Ɗan wasan gaba a Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, na dab da sa hannu a sabuwar yarjejeniyar tsawaita zamansa da ƙungiyar.
Barcelona ta dauki dan wasan tsakiyar kasar Mali Ibrahim Diarra me shekaru (17) daga Academia África Foot akan kwantiragi har zuwa 30 ga Yuni, 2028.
Kawo zuwa yanzu yan wasan da suka fi yawan zura kwallaye a Firimiya lig:
Erling Haaland – 13
Mohamed Salah – 13
Cole Palmer – 11
Bryan Mbeumo – 10
Wasu kafafen watsa labarai a Morocco na ta suka gami da nuna rashin jin dadinsu bayan da CAF ta bayyana Ademola Lookman a matsayin gwarzon dan wasan nahiyar Afirka na wannan shekarar.
Tun a daren jiya wajen bayar da kyautar, aka fara hango wasu fuskoki suna fita waje bayan an bayyana Ademola Lookman na Najeriya a matsayin dan wasa mafi hazaka a nahiyar Afirka a wannan shekarar.
Kuma rahotanni sun bayyana cewa fuskokin abokan tafiyar Achraf Hakimi ne, wadanda sun yi tsammanin shine zai lashe kyautar.
Indai kwallon kafa kake a nahiyar Afirka, Ademola Lookman shine shugabanka a wannan shekarar.