Fitaccen Ɗan wasan Real Madrid Jude Bellingham ya samu rauni a ƙafarsa yayin da ya ke atisaye a kulob ɗinsa, makonni biyu kafin Ingila ta fara gasar cin kofin UEFA Nations league.
Har yanzu dai a a tabbatar da tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinyar ba amma wasu rahotanni daga Sifaniya sun nuna cewa ba zai buga wasa ba har zuwa ƙarshen watan Satumba, wanda hakan zai hana shi buga wasanni biyu na farko da sabon kocin riƙon ƙwarya na Ingila Lee Carsley zai jagoranta.
Ingila za ta kara da Jamhuriyar Ireland a ranar 7 ga watan Satumba da kuma Finland a ranar 10 ga Satumba a gasar Nations League.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Real Madrid ta ce anyiwa Bellingham gwajin lafiya a ranar Juma’a akan raunin da ya ji a kafarsa ta dama kuma za a cigaba da sa ido kan lamarin.