Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gwamnan Kano Ya Mikawa Majalisa Sunayen Mutane Biyu Don Nada Su Kwamishinoni ‎
Afrika

Gwamnan Kano Ya Mikawa Majalisa Sunayen Mutane Biyu Don Nada Su Kwamishinoni ‎

September 28, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Abba Kabir Yusuf

‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni a cikin majalisar zartarwar jiharsa.
‎
‎Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
‎
‎Wadanda Aka Tura Sunayen su ne
‎
‎1. Barista Abdulkarim Kabir Maude (SAN designate)
‎Barista Maude, dan asalin karamar hukumar Minjibir, mai shekaru 40, ana sa ran zai karɓi kambun babban lauya na ƙasa (SAN) gobe Litinin a gaban Kotun Koli.
‎
‎Ya kammala karatunsa na farko a fannin lauya daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, sannan ya samu digiri na biyu a fannoni biyu — International Economic Law daga Maryam Abacha American University of Niger da Business Commercial Law daga Jami’ar Bayero Kano.
‎

‎Barista Maude ya shafe sama da shekaru 10 yana aiki a fannoni daban-daban na lauya, ciki har da shari’a, harkokin kasuwanci da kula da kadarori. Shi memba ne na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (Nigerian Bar Association) da kuma Chartered Institute of Arbitrators of Nigeria.
‎
‎2. Dr. Aliyu Isa Aliyu
‎Dr. Aliyu, mai shekaru 41, kwararre ne a fannin lissafi kuma mai shirin zama Farfesa. Ya karanci digirinsa na farko a Jami’ar Bayero Kano, ya samu digiri na biyu (Masters) daga Jordan University of Science and Technology, sannan ya yi digirin digirgir (Ph.D) a Firat University, Turkiyya.
‎
‎Ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Tarayya Dutse a shekarar 2014 kafin daga bisani ya koma North West University, Kano, inda yake matsayin Associate Professor. Haka kuma ya halarci horaswa a kasashen China da Cyprus.
‎‎Tun shekarar 2023, Dr. Aliyu yana rike da mukamin Babban Mai Kidayar Jama’a kuma Kakakin Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano. Shi ne daya daga cikin daliban da suka ci gajiyar tallafin karatun waje na Kwankwasiyya, sannan ya taba rike mukamin sakataren kudi na jam’iyyar NNPP a jihar.
‎
‎Sabon Solicitor-General
‎‎A wani bangare na sanarwar, Gwamna Yusuf ya kuma amince da nadin Barista Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Solicitor-General kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano.
‎
‎Kafin wannan nadin, Barista Tahir ya kasance Daraktan Mai Shigar da Kara (Public Prosecution) a ma’aikatar, inda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa.
‎
‎An umarci shugaban ma’aikata da ya tabbatar da kammala dukkan matakan gudanarwa domin sabon lauya ya fara aiki daga Litinin, 29 ga Satumba, 2025.
‎
‎“Za Mu Ci Gaba da Zabar Matasa Masu Kwarewa” – Gwamna Yusuf
‎
‎Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirinsa na ci gaba da zabar matasa masu basira, kwarewa da gaskiya domin kara inganta aikin gwamnati da samar da nagartaccen shugabanci a jihar.
‎
‎“Jihar Kano tana bukatar sabbin tunani da sabbin dabaru wajen gudanar da mulki. Wannan shi ne dalilin da ya sa muke bai wa matasa damar taka muhimmiyar rawa a gwamnati,” in ji Gwamna Yusuf.
‎

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamnan Kano ya sauke shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Abdullahi Musa daga mukaminsa

March 11, 2026

Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama – Ma’aikatar tsaro

March 10, 2026

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

March 9, 2026

Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

March 9, 2026

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

March 6, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.