Real Madrid na kara kaimi wajen zawarcin Alexander-Arnold amma Liverpool na fatan za ta shawo kan dan wasan mai shekaru 26 ya ci gaba da zama.
Dan wasan bayan na Liverpool Arnold, mai shekara 26, zai iya barin Anfield don komawa Real Madrid a kyauta, yayin da amininsa Jude Bellingham ke ta kokarin gamsar da shi ya yi hakan.
Jurgen Klopp ya zama sabon shugaban ƙwallon ƙafa na dukkan ƙungiyoyin rukunin Red Bull da ke faɗin duniya.
Jurgen Klopp zai fara aiki daga Janairun 2025 akan kujerar, wadda zata bashi damar bayar da shawarwari ga dukkan ƙungiyoyin Red Bull, kama daga kan masu horaswa, masana da kuma fagen saye da musayen ƴan wasanni.
Sannan a cikin tattaunawar Klopp ya shigo da yarjejeniyar da zata bashi dama domin ya zama mai horas da ƴan wasan Germany anan gaba.
Real Madrid ta yi imanin Vinícius Junior ne zai lashe kyautar Balland’or 2024 ranar 28 ga watan Oktoba.
Ƙungiyar tuntuni ta fara shirye-shiryen yin duk wasu abubuwa da yakamata ga ɗan wasan na Brazil da zarar ya lashe kyautar.
Dan wasan gaban Bournemouth Antoine Semenyo, mai shekara 24, yana jan hankalin Liverpool, da Newcastle United da Tottenham bayan dan wasan na Ghana ya fara taka leda a kakar wasa ta bana.
Cole Palmer ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Ingila na shekara ta 2023-24.
Sam C ya bayar da rahotan cewa, Michael Carrick ya buɗe kofa domin amincewa ya dawo Old Trafford.
Tsohon dan wasan tsakiya na United kuma kocin riko a baya yana son komawa kulob din a matsayin da ya dace.
Kwarewar Carrick da gadon sanin asalinsa na United sun sa shi ya zama ɗan takara mai ƙarfi domin kasancewa mai bada shawara a fagen horarwa.