Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » ‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu
Afrika

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da al’ummar Najeriya cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gina ƙasa mai dorewa, zaman lafiya, da wadata. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar mambobin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tsarin siyasa da tattalin arziƙin da suka daɗe suna dakushe ci gaban ‘yan ƙasa, yanzu ana musanya su da sabbin tsare-tsare da za su ba kowa damar cin moriyar arziƙin ƙasa. Ya kuma sha alwashin ci gaba da aiwatar da garambawul ɗin da nufin samar wa talakawa da marasa ƙarfi guraben ayyukan yi da sauƙin rayuwa.

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

“Kuna wakiltar lamirin al’ummar da ke son kakkabe sarƙar talauci da yanke ƙauna,” in ji shugaban sa’ilin da yake jawabi ga tawagar.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya kada su yarda da kalaman ɓata suna na ‘yan hamayya, inda ya ce idan ma ba su ganin ayyukan hanyoyi da gadoji da ake yi, to za a samar musu da gilashin gani don su gani da kyau.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, Gwamnoni da suka haɗa da na Yobe, Gombe, Kebbi, Ebonyi, Delta, Kogi, Ekiti, Benue, Taraba, Edo, da Kaduna, Tsofaffin Gwamnoni da Shugabannin Majalisa Kamar su Aminu Bello Masari, Ifeanyi Okowa, Tanko Al-Makura, da Anyim Pius Anyim.

A nasa jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yaba wa shugaban bisa ƙarfin halin aiwatar da sauye-sauyen da wasu shugabannin na baya suka kasa yi, musamman batun cire tallafin mai da haɗe farashin canjin kuɗi.

Masari ya tabbatar wa shugaban cewa jiga-jigan siyasar shiyyar Arewa maso Yamma suna bayansa ɗari bisa ɗari, kuma za su zagaya don duba ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi a shiyyar domin wayar da kan jama’a.

Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su ci gaba da isar da saƙon fatan alheri ga jama’a a matakin gundumomi da ƙauyuka, yana mai jaddada cewa “Najeriya tana hannun amintattu.”

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.