Tsohon Ministan Sadarwa , Farfesa Isa-Ali Pantami, ya bayyana cewa ya kamata masu rike da mukaman gwamnati su gabatar da sahihan bayanai da ke nuna irin ayyukan da suka yi, yana mai jaddada cewa tsabtataccen tarihinsa bayan barin mulki ya isa shaida.
Pantami ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a jihar Gombe yayin kaddamar da wani kundin bayanai da ke tattara manyan ayyuka guda 241 da kuma samar da damar ayyukan yi sama da 700 da aka aiwatar a lokacin mulkinsa.
An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo
Tsohon ministan, wanda ke neman zama gwamnan jihar Gombe, ya kalubalanci masu neman mukaman siyasa da su yi koyi da salon nasa ta hanyar nuna ainihin nasarorin da suka samu maimakon yin alkawura kawai.

