Real Madrid da Barcelona za su kara a wasan karshe a Spanish Super Cup a yau Lahadi a Saudi Arabia.
Real Madrid ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta doke Mallorca 3-0 ranar Alhamis a filin wasa na King Abdallah a karawar daf da karshe ta biyu.
Ita kuwa Barcelona ta kai wannan gurbin, saboda cin Athletic Club 2-0 da ta yi ranar Laraba a wasan daf da karshe na farko a dai Saudi Arabia.
Wannan shi ne wasan farko na El Clasico a 2025, karo na huɗu a jere da za su fafata a Spanish Super Cup.
Wannan wasan dama ce ga Barcelona ta ɗauki fansa kan Real Madrid, wadda ta lashe kofin na Spanish Super Cup a bara a kan ƙungiyar Camp Nou.
Shi kuwa Carlo Ancelotti na fatan zai rama doke shi 4-0 da Barcelona ta yi a bara a cikin watan Oktoba a La Liga a Santiago Bernabeu.
Kociyan Barcelona, Hansi Flick na fatan ɗaukar kofi a karon farko a ƙungiyar, wanda ya fara aiki kan fara kakar bana, wanda ya maye gurbin Xavi Hernandez.
Barcelona ce kan gaba a yawan ɗaukar Spanish Super Cup mai 14 jimilla, sai Real Madrid mai 13 da Athletic Bilbao da Deportivo La Coruna da kowacce keda uku.