Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Darakta janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), a kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an sace tsohon Shugaban NYSC din ne da karfe 12:30 na safiyar ranar Alhamis inda wasu mahara dauke da muggan makamai suka afkawa al’ummar garin, inda suka rika harbe-harbe a kai a kai domin sanya fargaba da tsoro a tsakanin mazauna yankin.
Daga bisani ne sukayi awan gaba dashi.
Har ya zuwa lokacin bayar da wannan rahoton hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.