Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi hasashen yuwar samun ruwa mai ɗauke da tsawa a faɗin kasar tun daga ranar Litinin, 23 ga Satumba zuwa Laraba 25. Hasashen wanda NiMet ta fitar a ranar Lahadi ya nuna cewa za a samu ruwan sama da safiyar Litinin a jihohin Sokoto da Kebbi da Borno. Haka kuma hukumar ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar samun ruwan sama a Jigawa da Taraba da Adamawa da Gombe da Bauchi da Kano da Katsina da Kaduna da Zamfara da Kebi da Sokoto a ranar Litinin ɗin da rana. “Akwai…
Author: Wafsym
Gwamnan Jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya bayyana alakar dake tsakanin Jihar Kano da Maiduguri da cewa tsohuwar alaka ce Mai tsohon tarihi. Gwamnan Babagana Zulum ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Gwamnati bisa rakiyar Shehun Borno Alhaji Abubakar ibn Umar Garbai El Kanemi a ziyar jajantawa da Sarkin Kanon ya Kai Jihar Borno. Gwamna Zulum ya godewa mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero bisa wannan ziyara da ya Kai musu inda yace bazasu taba mantawa da wannan ziyara ba…
Sabon shugaban hukumar Alhazan Nigeria NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ci alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da gudanar da aiki mai tsafta tare da kawo cigaba a hukumar. ‘’Tafiyar da hukumar alhazan Najeriya NAHCON aiki ne mai girman gaske dake bukatar tayani da addu’a domin na samu karfin gwiwar tafiyar da aikin cikin gaskiya da amana” inji Farfesa Pakistan. Shugaban hukumar ta NAHCON na wannan jawabin ne lokacin da gidauniyar cigaban Tudun Murtala dake jihar Kano a arewacin kasar ta kai masa ziyarar taya murna gidansa, bisa mukamin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bashi na…
Fitaccen Ɗan wasan Real Madrid Jude Bellingham ya samu rauni a ƙafarsa yayin da ya ke atisaye a kulob ɗinsa, makonni biyu kafin Ingila ta fara gasar cin kofin UEFA Nations league. Har yanzu dai a a tabbatar da tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinyar ba amma wasu rahotanni daga Sifaniya sun nuna cewa ba zai buga wasa ba har zuwa ƙarshen watan Satumba, wanda hakan zai hana shi buga wasanni biyu na farko da sabon kocin riƙon ƙwarya na Ingila Lee Carsley zai jagoranta. Ingila za ta kara da Jamhuriyar Ireland a ranar 7 ga watan Satumba da…
A ranar 11 ga watan Agusta ne, sabon zaɓaɓɓen shugaban na Iran Masoud Pezeshkian ya gabatar da sunayen mutanen da yake so a ba ministoci a gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman ƙuri’ar amincewa. Dangane da dokar Iran, kakakin majalisar ƙasar zai karanta takardar gabatarwa ta shugaban ƙasar, inda bayan haka sai sauran takardu su biyo baya waɗanda za a miƙa su ga kwamitocin da suka dace domin dubawa. Waɗannan kwamitocin an kafa su ne domin tantance cancanta da takardu da asali da kuma shawarar bayar da ma’aikatar da ta dace ga kowane minista tare da gabatar da bincikensu ga…
Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa da kuma jihar Imo dake kudancin kasar. A hukuncin da ta yanke ranar Juma’a Kotun ta tabbatar da Sanata Duoye Diri na jam’iyyar PDP, a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Bayelsa, bayan da ta yi watsi da ƙarar da Timipre Silva na jam’iyyar APC, ya shigar gabanta don ƙalubalantar nasarar da Mista Diri ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023. Haka kuma kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na APC a matsayin gwamnan jihar Kogi, bayan watsi da…
Gwamnan Jihar Kano dake arewacin Najeriya, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da katafariyar kasuwar shanu a karamar hukumar Dambatta domin bunkasa harkokin kasuwanci a jihar Kano. Gwamnan ya ce aikin kasuwar hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Kano da bankin raya Musulunci na Duniya. Har ilayau ya ce an samar da irin wadannan kasuwannin guda biyar awasu daga cikin Kananan hukumomin Kano duk da tallafin Bankin raya Musulunci. Haka zalika gwamnan ya kaddamar da hanya da ta tashi daga garin Dambatta zuwa garin Diggol, a wane mataki na yunkurin gwamnati na rage alummar yankin wahalhalun d ahanyar ka iya jawowa.…
Wasu manyan hanyoyin fita da shiga na birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar mai kimanin mutum miliyan 1.5 sun kusan katsewa baƙi ɗaya, kana sama da mazauna birnin mutum 11,500 ne iftila’in ambaliyar ruwan sama ya shafa. A watanni uku da suka wuce, ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 217 a faɗin ƙasar kana ta shafi sama da mutane 350,000, a cewar gwamnatin mulkin soji ta Nijar. Da farko dai birnin Yamai ya tsira daga sauran yankunan kudu maso yammacin Nijar, amma a yanzu, kwale-kwale ne suka maye gurbin ƙanana da manyan motoci da babura wajen jigilar mutane da kayayyaki a…
