Kamfanin mai na Dangote dake Najeriya ya sanar da cewa a karon farko ya fitar da man fetur zuwa kasar Kamaru, wanda ake sa ran hakan zai buɗe wata hanya da za ta taimaka wurin samun wadataccen man fetur da kuma daidaita farashi a yankin. Sai dai kamfanin na Dangote bai bayar da cikakken bayani kan ganga nawa ya fara fitarwa zuwa kasar ba. Kamfanin samar da makamashi na kasar Kamaru Neptune Oil a cikin wata sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa, duk kanin kamfanonin biyu suna nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin…
Author: Wafsym
A wata ganawa da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya jaddada aniyarsa na gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025 cikin tsari da nasara. Ahugaban ya bayar da tabbacin ne a jawabinsa yayin wani taro da aka gudanar a hedikwatar hukumar NAHCON da ke Abuja. Farfesa Pakistan ya nuna godiya ga Allah da ya ba da damar gudanar da taron tare da jaddada sadaukarwar hukumar wajan shawo kan kalubale da kuma sake mayar da hankali domin samun damar inganta aikin hukumar. A cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana kalubale da dama da ya tarar lokacin da…
Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya a duniya, da kimanin mutum biliyan biyu inda aka samu raguwar masu mutuwa daga cutar tun daga shekarar 2000 kawo yanzu. Sai dai rahoton ya ce har yanzu akwai miliyoyin mutane da ke fama da wannan cuta a duniya musamman a nahiyar Afirka, inda adadin masu kamuwa da cutar ya kai kashi 95 cikin dari, sakamakon rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da kuma hanyoyin samar da kariya daga cutar. Duk da wannan nasarar da aka…
Ana zargin wani matashi dan shekara 22 mai suna Godwin daga yankin Elebele a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa da cakawa mahaifiyarsa wuka bayan ya gaza samun nasarar amfani da ita wajen yin tsafi. A cewar wasu majiyoyi, mutumin da ake zargin ya dawo garin ne makonni kalilan da suka wuce bayan ya yi bulaguro na tsawon watanni a makwabciyar jihar inda ya je wajen wata matattara ta ‘yan Yahoo da ake kira da HK. Da yake tabbatar da lamarin, shugaban kungiyar matasa na kauyen Elebele, Kwamared Precious Okala, ya shaida wa manema labarai cewa an kira shi…
Shugaba Biden na Amurka ya kare ci gaban da ya samu a fanni tattalin arziki ya kuma ƙalubalanci gwamnatin Trump mai zuwa da ta ci gaba da inda ya tsaya. Da yake jawabi a Washington, Mista Biden ya yi tir da shirin Mista Trump na ɗora haraji kan manyan abokan kasuwancin Amurka, Mexico da Canada da kuma China. Yayin da ake ganin Mista Trump ya lashe zaɓen ne saboda tsadar rayuwa da ta yi wa Amurkawa dabaibayi, Shugaba Biden ya ce Mista Trump zai gaji tattalin arziki mafi ƙarfi a tarihin Amurka.
Shugaban ƙasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier na ziyarar aiki a Najeriya. Mista Steinmeier ya isa Najeriya ranar Talata da daddare, nda ya samu tarbar ministan Abuja, Nyesom Wike bayan saukarsa a filin jirgin saman Abuja. A ziyarar da ake sa ran ta kwana uku ce, Shugaban na Jamus zai gana da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da kuma shugaban hukumar Ecowas, Alieu Omar Touray a Abuja. Daga nan Mista Steinmeier zai wuce birnin Legas inda zai gana da wakilan kasuwanci da jami’an ƙungiyoyin fararen hula da na al’adu, ciki har da Farfesa Wole Soyinka, kamar yadda gidan Talbijin na Channels ya…
Mutanen da gwamnatin sojin Nijar ta kulle tun bayan hawa mulki. A makon nan ne ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta buƙaci gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da duk wasu zarge-zarge tare da sakin ɗan rajin kare hakkin bil’adama na ƙasar, Mousa Tchangari. Tchangari na daga cikin mutane na baya-bayan nan da gwamnatin mulkin sojin ta Nijar ta kama tare da tsarewa tun bayan hawa mulki a watan Yulin 2023. Sanarwar da Human Rights Watch ta fitar ta ce hukumomin tabbatar da ƴancin bil’adama kamar Amnesty International da World Organisation Against Torture “sun…
Akalla mutane 30 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a kauyukan Kastina-Ala da Logo na jihar Benue. Hare-haren wanda aka fara tun ranar Lahadi sun ci gaba har zuwa ranar Litinin, ana zargin makiyaya ne ɗauke da makamai daga ƙasashen waje ne suka kai su. A Ƙaramar Hukumar Kastina-Ala, an gano gawarwaki 10, yayin da aka kashe mutane 20 a Ƙaramar Hukumar Logo. Cif Joseph Anawah ya ruwaito cewa sama da mutane 300 dauke da makamai sun kai hari a unguwar Azege da safiyar Lahadi. Jami’an tsaron yankin sun cika makil har sai da wani jirgin soji ya…
Yayin da Duniya ke bikin zagayowa ranar yaƙi da muzgunawa ƴaƴa mata a wanan litinin ɗin, wani bincike da sashen yaki da cin zarafin ƴaƴa mata a Faransa ya wallafa, ya nuna cewa an samu ƙorafe-ƙorafen cin zarafin mata sau dubu 484 a shekara 2023 data gabata. Binciken wanda aka gudanar akan matasa sabbin tasowa waɗanda shekarunsu suke tsakanin 18 zuwa sama, ya shafi yankunan Guadeloupe da Martinique da kuma Reunion. Binciken ya nuna cewa a shekara guda mata dubu 123 akaci zarafinsu ta hanyar yin lalata da su, yayin da dubu 339 kuwa aka ci zarafinsu ta hanyar duka,…
Ministan Tsaron Nijeriya Mohammed Badaru Abubakar ya ce karshen ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Najeriya ya kusa, adaidai lokacin da kasar ke samun karin kayan aikin soja daga Turkiyya. Minista Badaru ya yi wannan jawabin ne a sansanin sojin saman Nijeriya da ke jihar Katsina a arewacin kasar, yayin kaddamar da jiragen yaki masu saukar ungulu na T129 ATAK guda biyu, wadanda kasar ta saya daga kasar Turkiyya. “Karshen ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan daba masu dauke da makamai a kasar ya kusa,” in ji Ministan Tsaron Nijeriya a wajen taron a farkon makon nan. Ya kuma…
