Yayin da Duniya ke bikin zagayowa ranar yaƙi da muzgunawa ƴaƴa mata a wanan litinin ɗin, wani bincike da sashen yaki da cin zarafin ƴaƴa mata a Faransa ya wallafa, ya nuna cewa an samu ƙorafe-ƙorafen cin zarafin mata sau dubu 484 a shekara 2023 data gabata.
Binciken wanda aka gudanar akan matasa sabbin tasowa waɗanda shekarunsu suke tsakanin 18 zuwa sama, ya shafi yankunan Guadeloupe da Martinique da kuma Reunion.
Binciken ya nuna cewa a shekara guda mata dubu 123 akaci zarafinsu ta hanyar yin lalata da su, yayin da dubu 339 kuwa aka ci zarafinsu ta hanyar duka, sai mata dubu 109 waɗanda maganganu marasa daɗi suka taba lafiyar kwakwalwasu.
Wanan dai na zaman adadi mafi muni da aka samu a Faransa cikin shekaru 10 suka gabata.
Sai dai binciken ya ce kashi 14 kawai ne na matan da aka ci zarafinsu su ka shigar da kara a wajan hukumomin da suka dace domin a bi musu haƙƙinsu.
Tun daga shekara 1945 Majalisa Ɗinkin Duniya, ta soma fitar da gargadi kan rashin samun daidaito tsakanin maza da mata a mutanen Faransa .