Akalla mutane 30 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a kauyukan Kastina-Ala da Logo na jihar Benue.
Hare-haren wanda aka fara tun ranar Lahadi sun ci gaba har zuwa ranar Litinin, ana zargin makiyaya ne ɗauke da makamai daga ƙasashen waje ne suka kai su.
A Ƙaramar Hukumar Kastina-Ala, an gano gawarwaki 10, yayin da aka kashe mutane 20 a Ƙaramar Hukumar Logo.
Cif Joseph Anawah ya ruwaito cewa sama da mutane 300 dauke da makamai sun kai hari a unguwar Azege da safiyar Lahadi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kastina-Ala, Justine Shaku, ya tabbatar da harin da aka kai a ƙauyen Adabo da matsugunan Tse Gwebe da sanyin safiyar Litinin ɗin nan, wanda ya janyo hasarar rayuka da sace-sace.
Clement Kav, Shugaban Ƙaramar Hukumar Logo, ya bayyana cewa maharan sun yi iƙirarin mallakar filin Tombo, wanda ya yi Sanadin Mutuwar Mutane 17 da jikkata 37.
An tura karin jami’an tsaro, kuma an samu zaman lafiya.