Author: Wafsym

Shugaban hukumar Alhaza Najeriya NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce yanzu haka hukumar ta na cigaba da kai ziyara jihohi da wajan wasu masu ruwa tsaki a faɗin ƙasar ne domin ƙarfafa shirye-shiryen da hukumar ke yi na tsara aikin Hajjin da ya dace a 2025 da kuma bayanta. Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana hakan ne ranar Juma’a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris a gidan gwamnatin jihar dake Birnin Kebbi. Farfesa Pakistan ya lissafo wasu sabbin matakai da hukumarsa ke ɗauka domin ragewa alhazai raɗaɗi a gida da kuma ƙasar Saudi Arabia. A cewarsa,…

Read More

Shugaban Karamar Hukumar Dala Ya Yi Kira Ga Masu Hannu Da Shuni Su Tallafawa Yunkurin Gwamnati Don Bunkasa Ilimi Da Lafiya Shugaban karamar hukumar Dala, Alhaji Surajo Ibrahim Imam, ya yi kira ga masu hannu da shuni da kamfanoni su tallafawa yunkurin gwamnati na bunkasa ilimi da lafiyar al’umma. Ya bayyana hakan ne yayin bikin bude dakunan gwajin kimiyya (laboratories) a makarantar mata ta GGC Dala, wanda aka gudanar tare da halartar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi II. Dakunan gwajin da aka kaddamar sun hada da: Chemistry Laboratory mai suna Gwamna Eng. Abba Kabir Yusuf, Physics Laboratory…

Read More

Matatar mai ta Dangote ta sanar da karya farashin litar man fetur zuwa 899.50 Mai magana da yawun rukunin Kamfanonin Dangote Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar yau Alhamis. Inda ya ce an rage farashin fetur daga N970 zuwa N899.50 domin mutane su samu sauƙin tafiye-tafiye a lokutan bukukuwan ƙarshen shekara. A watan Nuwambar da ya gabata ma, matatar man mai zaman kanta a Najeriya ta rage farashin litar man zuwa naira 970. Chiejina ya ƙara da cewa matatar ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama’ar Najeriya man fetir mai inganci kuma cikin…

Read More

Shugaban majalisar wakilan Najeriya Tajuddeen Abbas, ya ce matakan da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu yake ɗauka wajen inganta tattalin arzikin Najeriya na nuna yadda shugaban ya damu da damuwar al’ummar ƙasar. Abbas ya bayyana hakan ne a jawabinsa a lokacin da shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a gabatan majalisar dokokin ƙasar a ranar Laraba. “Majalisar dokoki za ta ci gaba da goyon bayan matakan gyare-gyaren da kake ɗauka ta hanyar yin dokoki da kuma tattaunawa tare da wayar da kan mutane domin ƙara fahimta da amincewa” Inji Abbas Ya ƙara da cewa tafiye-tafiyen da shugaban yake…

Read More

NBS ta ce an biya kuɗaɗen fansar ne tsakanin watan Mayu na shekarar 2023 zuwa watan Afrilun shekarar 2024. Rahoton ya ƙara da cewa kashi 65 cikin 100 na gidajen da iftila’in garkuwa da mutane ya shafa sun biya kuɗin fansa domin a saki ‘yan’uwansu. A rahoton da hukumar ta fitar ranar Talata game da laifuka da kuma yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a Nijeriya, ta ce masu garkuwa da mutane sun kashe fiye da mutum 600,000 sannan suka sace fiye da mutum miliyan biyu a faɗin Nijeriya tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. “Matsaƙaicin kuɗin fansar da…

Read More

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa wa’adin kasafin kuɗin shekarar 2024 kai har zuwa ranar 25 ga watan Yuni, 2025. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a zauren Majalisar Dokokin Ƙasa. Akpabio, ya bayyana cewa kasafin 2024 ya samu nasarar kashi 50 na ayyukan manyan gine-gine da kuma kashi 48 na kuɗin tafiyar da gwamnati. Shugaba Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 domin tantancewa da yin nazari.

Read More

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewar har yanzu cutar malaria ko kuma zazzabin cizon sauro na ci gaba da illa a wasu kasashen duniya sakamakon alkaluman da ta gabatar wanda ya nuna cewar akalla mutane miliyan 263 suka harbu da ita a shekarar 2023, yayin da dubu 597 suka sheka lahira. Sanarwar da kungiyar kawancen Gavi dake yaki da cututtuka ya gabatar, ya ce alkaluman Majalisar dinkin duniya ya nuna cewar an samu karuwar akalla mutane miliyan 11 da suka harbu da cutar daga cikin adadin da aka samu a shekarar 2022, yayin da adadin wadanda suka mutu kuma ke…

Read More

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai gaskiya da amana da tsananin tausayin talakawa. Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar da tsohon shugaban yake murnar cika shekara 82 a Duniya. Garba Shehu ya ce, “Buhari shugaba ne daban, wanda yake damuwa da damuwar talakawa da masu rauni, sannan yake dagewa wajen inganta rayuwar talakawa da fitar da su daga cikin ƙunci.” Garba Shehu ya ce siyasa da cin hanci da rashawa ɗanjuma ne da ɗanjumai a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya. “Tunanin mutane shi ne duk…

Read More

Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ingila ta dakatar da ɗan wasan Chelsea Mykhailo Mudryk daga buga wasa zuwa wani ɗan lokaci, bisa zarginsa da ta’ammali da ƙwayoyi. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta tabbatar da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ingila ta tuntuɓeta akan dan wasanta Mykhailo Mudryk game da zargin da ake yi masa na yin amfani da ƙwayoyi ba bisa ka’ida ba. Hukumar ta Gano Hakan ne bayan gwajin fitsari da aka yi masa tare da wasu ƴan wasa. “Dukkan kungiyar mu har da Mykhailo Mudryk muna ba da cikakken goyon baya ga hukumar kwallon kafa ta Ingila…

Read More

Majalisar zartarwar Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar, Bola Tinubu ta sanar da cewa za ta tafi hutu daga ranar 18 ga watan Disamban 2024 zuwa 6 ga watan Janairun 2025. Majalisar ta bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da ta gudanar yau Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. A bayanin bayan taron majalisar, hakan na nufin ba za a gudanar da wani taron majalisar ba a tsawon lokacin da za ta kwashe tana hutu. Majalisar zartaswar Najeriya ta ƙunshi shugaban ƙasa da mataimakinsa da kuma ministoci. Sanarwar da majalisar ta fitar ta nuna cewa a taron na yau…

Read More