Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane dubu 597 a shekarar 2023 – WHO
Afrika

Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane dubu 597 a shekarar 2023 – WHO

December 17, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewar har yanzu cutar malaria ko kuma zazzabin cizon sauro na ci gaba da illa a wasu kasashen duniya sakamakon alkaluman da ta gabatar wanda ya nuna cewar akalla mutane miliyan 263 suka harbu da ita a shekarar 2023, yayin da dubu 597 suka sheka lahira.

Sanarwar da kungiyar kawancen Gavi dake yaki da cututtuka ya gabatar, ya ce alkaluman Majalisar dinkin duniya ya nuna cewar an samu karuwar akalla mutane miliyan 11 da suka harbu da cutar daga cikin adadin da aka samu a shekarar 2022, yayin da adadin wadanda suka mutu kuma ke kankankan a tsakanin shekarun biyu.

Wani abin tada hankali shi ne yadda akasarin wadanda suka mutu, wadanda yawansu ya kai kashi 95 na alkaluman da aka gabatar, ya nuna cewar daga Afirka suka fito, abinda ya sa shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Ghebreyesus ya yi kirar daukar matakan gaggawa domin tinkarar matsalar.

Ghebreyesus yace babu dalilin da zai sa wani mutum ya mutu sakamakon wannan cutar wadda ke ci gaba da illa da kuma kassara jama’a a yankin Afirka, musamman mata masu juna biyu da kuma kananan yara.

Shugaban hukumar lafiyar ya ce ya zuwa watan Nuwambar da ta gabata, an tabbatar da cewar kasashen duniya 44 sun yi nasarar kawar da cutar malariar baki daya daga cikin su, ya yin da wasu kuma ke ci gaba da daukar matakan cimma irin wannan nasarar.

Jami’in yace daga cikin kasashen duniya 83 da cutar tafi kamari a cikin su, 25 sun bayyana samun raguwar masu kamuwa da cutar, sabanin guda 4 kacal da aka gani a shekara ta 2000.

Ofishin hukumar lafiya ta duniya dake kula da Afirka ya ce alkaluma sun nuna raguwar kashi 16 na yawan mutanen da cutar ke hallakawa tun daga shekarar 2015.

Hukumar lafiyar ta ce kasashe 11 da suka fi samun masu fama da cutar sun gudanar da taro a wannan shekarar inda suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar taka rawa wajen magance illar da cutar keyi, kuma sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da kuma Ghana.

Sauran sun hada da Ghana da Mali da Mozambique da Nijar da Najeriya da Sudan da Tanzania da kuma Uganda.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026

NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano ‎

February 12, 2026

Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A kaduna  ‎

February 12, 2026

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf A Matsayin Shugaban NAHCON

February 11, 2026

Mata sun fi maza yin aikin baban-giwa a Najeriya

February 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Na Ajiye Shugabancin NAHCON – Abdullahi Saleh Pakistan

February 11, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

By WafsymFebruary 12, 2026

A daidai lokacin da ya rage ‘yan kwanaki kaɗan a shiga watan Ramadan mai alfarma,…

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

January 21, 2026

‎Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida Don Kare Rayukansu

January 19, 2026

‎Sauyin Yanayi Na Canza Yanayin Sanyi A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Masana ‎

January 18, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.