Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na shirin kai ziyara kasashen Ethiopia da Somaliya a cikin watanni biyu na farkon sabuwar shekarar 2025. Erdogan ya shaida wa wani taron matasa a lardin gabashi na Erzurum a ranar Asabar cewa an samu nasarar ne bayan “wani zama da ya kai sa’o’i bakwai.” Tare da haɗin kan ƙasashen biyu, “mun rattaɓa hannu (kan yarjejeniyar), kuma mun kammala aikin,” in ji shi. Wannan na zuwa ne bayan wata sasantawa ta tarihi, wadda Turkiyya ta jagoranta kuma ta kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu ga me da samun hanyar zuwa Bahar Maliya. A halin…
Author: Wafsym
Yau litinin a birnin Marrakesh na kasar Morroco, hukumar ƙwallon Afrika CAF za ta bayyana gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afrika na 2024. Daga cikin wadanda ke takara akwai Achraf Hakimi Morocco da Ademola Lookman daga Nigeria sai Serhou Guirassy da Rowen Williams da kuma Simon Andingra.
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta ECOWAS ta amince da ficewar Mali da Nijar da kuma Burkina Faso daga cikinta. Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne a babban taron ta na ƙoli da shugabannin ƙungiyar suka gudanar a Abuja. Jagororin ƙungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ɗin sun nuna amincewa da buƙatar da ƙasashen uku suka miƙa musu na janyewa daga ƙungiyar daga ranar 29 ga watan Janairu na 2025 da ke tafe. Haka kuma shugabannin ƙungiyar sun amince da naɗa shugaban Togo da na Senegal domin su cigaba da tattauna wa da ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso har…
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da sunayen mutane 6 zauren majalissar dokoki ta Kano domin tantancewa don Nada su mukamin kwamishina kuma Yan majalissar zartarwar Sa. Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da gwamnan ya aikewa kakakin majalissar Wanda kuma ya karanto yayin zaman majalissar na Yau. Daga cikin wadanda za’a nada mukamin kwamishinan akwai Shehu Wada Sagagi, Ismail Danmaraya, Dahiru Hashim Muhammad, Gaddafi Sani Shehu, Abdulkadir Abdussalam da kuma Ibrahim Wayya. Zauren majalissar ya bukaci wadanda za’a Nada dasu gaggauta aikewa zauren majalissar kwafin takardur su kafin tashi daga aiki a yau. Sannan zauren…
Tsohon gwamnan na jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan lokacin da ya ke tsokaci game da kiraye-kirayen mayar da mulkin Najeriya wani ɓangaren ƙasar a hirar sa da gidan talabijin na Channels. Ya kuma ce kamata ya yi jam’iyyu su fitar da tsari mai kyau na zaɓen wanda ya fi cancanta a tsakanin ƴan takara, da hakan zai bai wa al’uma damar zaɓin shugaban kasar da ya fi cancanta a tsakanin su. Daga nan Malam Ibrahim Shekarau ya ce duk da haka zai fi kyau al’uma su mayar da hankali wajen zaɓen shuwagabanni na gari da za su…
Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za su gana yau Lahadi a Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai da tsaro da kuma tattalin arzikin yankin. Ana sa ran batun ficewar ƙasashen yankin Sahel daga ƙungiyar ne zai zama babban ajandar taron na yau. Ƙa’idar da Ecowas ta gindaya ta sanarwar shekara guda kafin ficewar ƙasa daga ƙungiyar – wanda ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka yi – zai cika a watan Janairu mai zuwa. A makon da ya gabata ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida wa shugaban Jamus da ya ziyarci ƙasar, Frank-Walter…
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa fitaccen tauraron fina-finan Hausa na Kannywood, Sani Musa Danja a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni. Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwaman jihar Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamnan ya amince da naɗin Sani Danja tare da wasu mutane da shugabannin hukumomin da aka sauya wa ma’aikatu da masu bai wa gwamna shawara. A mako mai ƙarewa ne dai gwamnan na jihar Kanon ya yi wa majalisar zartarwarsa garambawul, inda ya sauke wasu ƙusoshin gwamnatinsa, cik har da sauke…
A yau ne 15 ga watan Disamba, kuma masoya shayi a faɗin duniya ke bikin ranar shayi ta duniya. A nan Kano, wasu masu sha da sana’ar shayi na gudanar da bikin ranar cikin farin ciki, inda masu sayar da shayi da masu ta’ammala da shi suka taru domin karrama wannan abin sha da zukata ke matuƙar so. Ranar shayi ta duniya, wadda majalisar ɗinkin Duniya ta samar a shekarar 2019, ana bikin murnar ranar ne a matsayin wata al’ada kuma abun bun ƙasa tattalin arziƙi. A birnin Kano, wasu masu sana’ar shayi sun ce su na sane da bikin…
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun. Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP tare da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, sun gana da Obasanjo a gidansa da ke birnin Abeokuta. Cikin wani saƙo da tsohon gwamnan na jihar Kano, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce a lokacin ganawar sun tattauna abubuwan da suka shafi ƙasa, ciki har da makomar siyasar ƙasar. “Mun yaba da yadda Baba ya nuna mana karimci da cikakken goyon baya,” kamar yadda ya wallafa.
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi maraba da sulhun da aka yi tsakanin Kasashen Ethiopia da Somalia wanda Turkiyya ta jagoranta a birnin Ankara. An gudanar da taron sulhun ne a ranar Laraba. Turkiyya ta jagoranci sulhun ne tsakanin ƙasashen biyu da ke maƙwabtaka da juna bayan sun kwashe kusan shekara guda suna tayar da jijiyoyin wuya. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya karɓi baƙuncin Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ranar Laraba, ya bayyana sulhun a matsayin wanda ke cike da “tarihi.” A ranar Alhamis, Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya…
