Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP tare da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, sun gana da Obasanjo a gidansa da ke birnin Abeokuta.
Read also: Kano Police Engage Youths, Civil Society Groups on Peaceful Elections
Read also: Rundunar ’Yan Sandan Kano Ta Tattauna Da Matasa Kan Zaman Lafiya A Lokacin Zaɓe
Cikin wani saƙo da tsohon gwamnan na jihar Kano, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce a lokacin ganawar sun tattauna abubuwan da suka shafi ƙasa, ciki har da makomar siyasar ƙasar.
“Mun yaba da yadda Baba ya nuna mana karimci da cikakken goyon baya,” kamar yadda ya wallafa.

