Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na shirin kai ziyara kasashen Ethiopia da Somaliya a cikin watanni biyu na farkon sabuwar shekarar 2025.
Erdogan ya shaida wa wani taron matasa a lardin gabashi na Erzurum a ranar Asabar cewa an samu nasarar ne bayan “wani zama da ya kai sa’o’i bakwai.” Tare da haɗin kan ƙasashen biyu, “mun rattaɓa hannu (kan yarjejeniyar), kuma mun kammala aikin,” in ji shi.
Wannan na zuwa ne bayan wata sasantawa ta tarihi, wadda Turkiyya ta jagoranta kuma ta kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu ga me da samun hanyar zuwa Bahar Maliya.
A halin yanzu shugaban na Turkiyya yana shirin kai ziyara Ethiopia da Somaliya tsakanin watannin Janairu da Fabrairun shekara mai zuwa.
Bayan ganawa da Erdogan a Ankara babban birnin Turkiyya a ranar Laraba, shuagabannin Somaliya da Ethiopia sun fitar da wata sanarwa ta haɗaka wadda aka yi wa laƙabi da “Sanarwar Ankara”, inda suka “sake tabbatar da mutunta ‘yancin kai da haɗin-kai da kuma kan iyakokin junansu.”
Da aka tambaye shi game da rawar da Turkiyya ta taka wajen samar da haɗaka, Erdogan ya bayyana cewa dangantakar Ankara mai ƙarfi da ƙasashen ta ba ta damar ci gaba da shiga tsakani yayin da sauran ƙasashe suka kasa.