Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta ECOWAS ta amince da ficewar Mali da Nijar da kuma Burkina Faso daga cikinta.
Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne a babban taron ta na ƙoli da shugabannin ƙungiyar suka gudanar a Abuja.
Jagororin ƙungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ɗin sun nuna amincewa da buƙatar da ƙasashen uku suka miƙa musu na janyewa daga ƙungiyar daga ranar 29 ga watan Janairu na 2025 da ke tafe.
Haka kuma shugabannin ƙungiyar sun amince da naɗa shugaban Togo da na Senegal domin su cigaba da tattauna wa da ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso har zuwa cikar wa’adin da nufin ba su haƙuri ko zasu aminta su sauya matsaya domin komawa cikin ƙungiyar.
Haka kuma ƙungiyar ta ECOWAS a zaman da ta yi a ranar Lahadi 15 ga Disamba ta amince a kafa wata kotu ta musamman domin yin hukunci dangane da laifukan da aka aikata a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Gambia Yahya Jammeh.
Ƙasashen na Mali da Burkina Faso da Nijar ba su tura ko da wakili ɗaya a yayin taron da aka gudanar a Abuja ba.
Sai dai a ranar Juma’a shugabannin ƙashen uku sun yi taron nasu a Yamai babban birnin Nijar inda a nan ne ma suka jaddada cewa “ba za su koma ƙungiyar ECOWAS ba”.
Bayan kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun bayyana matakin ficewa daga kungiyar, ECOWAS ta nada shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a matsayin mai shiga tsakani da zai jagoranci tattaunawa da kasashen uku da suka kafa Sahel Alliance.