Tsohon gwamnan na jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan lokacin da ya ke tsokaci game da kiraye-kirayen mayar da mulkin Najeriya wani ɓangaren ƙasar a hirar sa da gidan talabijin na Channels.
Ya kuma ce kamata ya yi jam’iyyu su fitar da tsari mai kyau na zaɓen wanda ya fi cancanta a tsakanin ƴan takara, da hakan zai bai wa al’uma damar zaɓin shugaban kasar da ya fi cancanta a tsakanin su.
Daga nan Malam Ibrahim Shekarau ya ce duk da haka zai fi kyau al’uma su mayar da hankali wajen zaɓen shuwagabanni na gari da za su yi wa ƙasa aiki.