Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da sunayen mutane 6 zauren majalissar dokoki ta Kano domin tantancewa don Nada su mukamin kwamishina kuma Yan majalissar zartarwar Sa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da gwamnan ya aikewa kakakin majalissar Wanda kuma ya karanto yayin zaman majalissar na Yau.
Daga cikin wadanda za’a nada mukamin kwamishinan akwai Shehu Wada Sagagi, Ismail Danmaraya, Dahiru Hashim Muhammad, Gaddafi Sani Shehu, Abdulkadir Abdussalam da kuma Ibrahim Wayya.
Zauren majalissar ya bukaci wadanda za’a Nada dasu gaggauta aikewa zauren majalissar kwafin takardur su kafin tashi daga aiki a yau.
Sannan zauren majalissar ya bukaci dasu hallara a gobe domin tantance Su.