Author: Wafsym

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta ƙara buɗe hanyoyin samun bashi ga ‘yan ƙasar tare da masana’antu domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar a cikin sabuwar shekarar 2025. A jawabinsa ga ‘yan ƙasar wanda ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi wannan ne ta hanyar kafa wani kamfani da zai kasance asusun tabbatar da biyan bashi na ƙasa wato National Credit Gurantee Company domin rage hatsarin ba da bashi ga bankuna da kamfanoni. “Kamfanin da ake sa ran zai fara aiki kafin tsakiyar shekara zai kasance na haɗin-gwiwa ne tsakanin ma’aikatun gwamnati…

Read More

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ɓarayin man fetur a yankin Neja Delta a yayin da take shirin fitar da gangar mai miliyan 3 a kowace rana a shekarar 2025. Nijeriya wadda ke cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen fitar da ɗanyen fetur a Afirka, ta na samun yawancin kuɗin shigarta daga mai, kuma tana samun fiye da kashi 90 na kuɗaɗen ƙasashen waje daga sayar da man fetur, amma tana fama da ɓarayin mai. A yayin da gwamnatin ƙasar ta yi ƙiyasin fitar da ganga miliyan 2.06 ta man fetur a kasafin kuɗinta na shekara mai…

Read More

Barcelona ta kara yin rashin nasara karo na biyu a ɗaukaka kakar yi wa ɗan wasan tawagar Sifaniya, Dani Olmo rijista kafin 1 ga watan Janairun 2025. Cikin watan Agusta, Barcelona ta sayi ɗan ƙwallon daga RB Leipzig mai buga Bundesliga kan £51m. To sai dai Barcelona ta yi masa rijista zuwa rabin kakar bana, saboda kar ta karya dokar kashe kudi daidai samu ta hukumar La Liga. Wata kotu ce ta hana Barcelona kara yi wa Olmo rijista a makon jiya, sannan a karo na biyu ta jaddada hukunci ranar Litinin. Hakan na nufin Olmo ba zai sake buga…

Read More

Gwamnatin Kano ta fara kwashe ‘dubban’ yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar. Gwamnatin ta fara ɗaukar matakin ne a jiya Litinin, inda ta samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran. Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce “mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni.” “Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba,” in…

Read More

Mayakan kungiyar Houthi dake ƙasar Yemen ta ce sun kai hari da makamai masu linzami biyu a filin jirgin saman Isra’ila, awanni bayan rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kakkaɓo wani makami da suka harba mata. “Makami na farko (da aka harba) ya nufi Filin Jirgin Saman Ben Gurion Airport” aTel Aviv, yayin da makami na biyu ya nufi wata tashar samar da hasken lantarki da ke kudancin Birnin Ƙudus, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar Houthi ta fitar. Kazalika ƙungiyar ta ce ta kai hari kan babban jirgin ruwan Amurka mai suna USS Harry S. Truman wanda ke ɗaukar…

Read More

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar farin cikinsa bisa sake bude matatar man fetur ta garin Warri da Kamfanin Mai na Ƙasar NNPCL ya yi a ranar Litinin, inda ya bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara a shekarar 2024 da ta ƙarawa ‘yan Nijeriya samun fatan alheri a gwamnatinsa. A ranar Litinin ne, matatar mai ta Warri ta koma aiki makonni bayan kamfanin NNPCL ya sake fara aikin tace gangar danyen fetur 60,000 a kowace rana a matatar Port Harcourt a watan Nuwamba. Gwamnatin Nijeriya ta ce a ranar Litinin ta koma wasu ayyuka a matatar mai…

Read More

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi fatali da zarge-zargen da shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi kan cewa Nijeriya da Faransa suna ƙoƙarin tayar da hargitsi a ƙasarsa. Sanarwa da Ministan yada Labaran gwamnatin Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar ranar Alhamis ta ce “Wadannan zarge-zarge dai sun wanzu ne kawai a tunani, domin Nijeriya ba ta taba kulla wata alaka da a bayyane ko a boye da Faransa ba – ko wata kasa – domin daukar nauyin hare-haren ta’addanci ko ta da hargitsi a Jamhuriyar Nijar sakamakon sauyin mulkin da aka samu a shugabancin kasar.” Sanarwar ta ci…

Read More

Akwai yiwuwar a sabuwar shekarar 2025 kamfanonin sadarwa a Najeriya su samu amincewar hukumar da ke kula da harkokin sadarwa NCC domin su ƙara kuɗin kiran waya da na data. Wani babban jami’i wandada ya buƙaci a sakaya sunanshi ya ce hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ka iya bai wa kamfanonin damar ƙara kuɗin. Rahotanni sun ce duk da tsadar rayuwa amma anƙi amincewa kamfanonin su ƙara kuɗin kira sama da shekaru 11 da suka gabata. Kamfanoni kamar MTN da Airtel da 9Mobile sun jima suna miƙa buƙatar ƙarin kuɗin ga Hukumar duba da yanayin tattalin arziki a ƙasar. Wasu…

Read More

A Ranar Litinin da ta gabata da maraice Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi tattaunawarsa ta farko da ‘yan jarida tun bayan da ya karɓi ragamar mulkin ƙasar a watan Mayun shekarar 2023. A cikin tattaunawar da aka yada a gidan talabijin na ƙasar, shugaban ya amsa tambayoyi da dama ciki hadda abubuwan da suka fi ci wa ‘yan ƙasar tuwo a ƙwarya. Cire tallafi man fetur da dala Da aka tambaye shi game da yadda ya ji ganin irin tasirin da cire tallafin ya yi kan tattalin arzikin ƙasar, Shugaba Tinubu ya ce babu wata hanya da ƙasar…

Read More

Gwamnatin Nijeriya ta janye dokar hana haƙar ma’adinai da ta sanya a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar bayan shekaru biyar da kafa dokar. Ministan haɓaka harkokin ma’adinai, Dele Alake, shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai tare kuma da shafinsa na X ranar Lahadi. Alake ya ce Nijeriya “za ta ci riba mai yawa idan aka ƙara farfaɗo da harkokin tattalin arziƙi a jiha mai ma’adinai da yawa kamar Zamfara wadda take da zinari da lithium da tagulla da yawa.” “Gwamnatin Tarayya ta ɗage dokar da ta hana haƙar ma’adinai a jihar Zamfara saboda ƙarin sauƙi…

Read More