Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gyara matatar man fetur ta Warri zai kara wa ‘yan Nijeriya ƙwarin gwiwa kan alƙawuranmu – Bola Tinubu
Afrika

Gyara matatar man fetur ta Warri zai kara wa ‘yan Nijeriya ƙwarin gwiwa kan alƙawuranmu – Bola Tinubu

December 31, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar farin cikinsa bisa sake bude matatar man fetur ta garin Warri da Kamfanin Mai na Ƙasar NNPCL ya yi a ranar Litinin, inda ya bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara a shekarar 2024 da ta ƙarawa ‘yan Nijeriya samun fatan alheri a gwamnatinsa.

A ranar Litinin ne, matatar mai ta Warri ta koma aiki makonni bayan kamfanin NNPCL ya sake fara aikin tace gangar danyen fetur 60,000 a kowace rana a matatar Port Harcourt a watan Nuwamba.

Gwamnatin Nijeriya ta ce a ranar Litinin ta koma wasu ayyuka a matatar mai ta Warri bayan rufe ta na tsawon kusan shekaru goma.

A saƙon da ya fitar bayan sanar da sake bude matatar da aka gyara, Shugaba Tinubu cikin kwarin gwiwa ya ce matatar mai ta Warri wadda yanzu tana aiki da kashi 60% cikin 100, na ba da tabbacin cewa shirin gwamnatinsa na ingancin makamashi da tsaro gaba daya suna kan hanya.

Ya kuma yaba wa mahukuntan NNPC karkashin jagorancin Mele Kyari kan yadda suke aiki tukuru domin dawo da martabar Nijeriya a matsayin babbar kasa mai arzikin man fetur.

“Na yi farin ciki da cewa kamfanin NNPCL yana aiwatar da umarnina na maido da dukkan matatun manmu guda hudu zuwa kyakkyawan yanayin aiki.

“Gyaran matatar mai ta Warri a yau ya sanya ni farin ciki ni da ‘yan Nijeriya. Wannan abu zai kara karfafa fata da bai wa ‘yan Nijeriya ƙwarin gwiwa na samun makoma mai kyau na alkawuran da muka yi musu.

“Wannan ci gaban wata babbar hanya ce ta rufe wannan shekara bayan wannan aikin da aka yi musamman idan aka hada da gyara tsohuwar matatar Port Harcourt da aka yi duk cikin shekarar nan.

Tun da fari gwamnati ta yi alkawarin farfado da matatun man da suka lalace saboda rashin kulawa.

Mele Kyari, shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, a lokacin da ya ziyarci cibiyar tare da jami’an gwamnati, da da ‘yan jarida ya ce, “Wannan kamfanin yana aiki a yanzu. Ba mu kammala shi 100 bisa 100 ba.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.