Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi fatali da zarge-zargen da shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi kan cewa Nijeriya da Faransa suna ƙoƙarin tayar da hargitsi a ƙasarsa.
Sanarwa da Ministan yada Labaran gwamnatin Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar ranar Alhamis ta ce “Wadannan zarge-zarge dai sun wanzu ne kawai a tunani, domin Nijeriya ba ta taba kulla wata alaka da a bayyane ko a boye da Faransa ba – ko wata kasa – domin daukar nauyin hare-haren ta’addanci ko ta da hargitsi a Jamhuriyar Nijar sakamakon sauyin mulkin da aka samu a shugabancin kasar.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa Shugaba Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya nuna jagoranci na gari, “tare da bude kofofin kananan ƙungiyoyin yanki domin sake shigar jamhuriyar Nijar cikin al’amura duk da halin da kasar ke ciki a siyasance.
“Nijeriya na ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma alakar diflomasiya mai dimbin tarihi da Nijar,” in ji sanarwar gwamnatin.
Tun da fari Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ne ya fada a wata hira da kafar yada labaran kasarsa cewa sun jima da bai wa gwamnatin Nijeriya bayanan sirri game da yadda Faransa take shirin kafa sansanin ‘yan ta’adda na ƙungiyar Lakurawa a arewacin Nijeriya.
Janar Tiani ya yi zargin cewa gwamnatin Nijeriya na da masaniya game da ayyukan Lakurawa da kuma yin watsi da shawarwarin da suka ba ta game da ‘yan ta’addan.
Minista Mohammed Idris ya ƙara da cewa Rundunar Sojin Nijeriya tare da hadin guiwar takwarorinta na rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, na samun nasarar dakile ayyukan ta’addanci a yankin.
“Don haka, shirme ne a ce Nijeriya za ta hada baki da duk wani karfi na kasashen waje domin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron wata kasa makwabciyarta.”
Tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a shekarar 2023 alaƙa tsakanin ƙasashen biyun maƙwabtan juna ke ta yin tsami, lamarin da har ya kai ga Nijar barazanar ficewa daga ƙungiyar ECOWAS, wadda Tinubu na Nijeriya ke jagoranta.
Maitaimakawa shugaban Najeriya kan harkokin yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz shima ya ce babu gaskiya a zarge zargen shugaban na Niger.