Kwamitin Aikin Hajji da Shugaban Ghana John Dramni Mahama ya kafa domin sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin bana ya sanar da rage kuɗin Aikin Hajjin daga GH¢75,000 zuwa GH¢62,000. Kwamitin ya bayyana cewa an rage kuɗin Aikin Hajjin ne domin cika alƙawarin da Shugaba John Dramani Mahama ya ɗauka domin sauƙaƙa wa musalman kasar. Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa an samu nasarar wannan rangwamen ne bayan da shugaban ƙasar ya aika wata tawaga zuwa ƙasar Saudiyya, domin sabunta tattaunawa da mahukuntan ƙasar kan tsare-tsaren aikin hajjin bana ciki har da batun kuɗaɗe. A yayin da yake magana kan…
Author: Wafsym
Ana zargin Jami’an tsaro da harbe mutane huɗu tare da jikkata wasu 16, yayin atisayen rushe gine-gine da gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta gudanar a garin Rimin Zakara, dake kusa da Jami’ar Bayero ta Kano a ƙaramar hukumar Ungogo a jihar. Aikin na rusau ɗin ya shafi gine-gine kimanin 18. Al’amarin ya faru ne adaren lahadi, lamarin da ya haifar da turjiya daga mazauna yankin, inda suka ce ba a basu isasshiyar sanarwa ba kafin rushewar. Malam Sunusi Dan-Baba, ganau ne ya shaida cewa tawagar rusau ta iso da daddare, inda suka fara ruguza gidaje da shaguna. Ya…
Jawabin farko na wa’adin mulkin Shugaba Donald Trump na biyu ya ƙunshi batutuwa kamar yadda yayi a jawabin wa’adinsa na farko: gama-garin suka ga ƙasar da ya karɓi ragamar mulkinta da kuma manyan alƙawurra na magance matsalolin. Shekaru takwas da suka gabata, Donald Trump ya bayyana abin da ya kira “lalata Amurka ” kuma ya yi alƙawarin kawo ƙarshensa nan-take. A ranar Litinin, ya bayyana cewa “faɗuwar” ƙasar za ta zo ƙarshe nan-take, lamarin da zai kawo “lokacin da Amurka za ta fi kyau a tarihi.” Matsalolin duniya “Wata guguwar canji tana kaɗawa faɗin ƙasar. Haske na bazawa kan duniya…
Gwamnatin jihar Katsina dake Arewacin Najeriya ta musanta batun cewa ta fara shiga sasanci da ƴanbindigar jihar, inda ta ce ko kusa babu hannunta a ciki. Gwmanatin ta bayyana hakan ne bayanda wasu jagororin ƴanbindiga suka miƙa bindigogi da mutanen da suka yi garkuwa da su ga sojoji a jihar. Kwamishinan yada labaran jihar Katsina, Dr. Bala Salisu ya ce gwamnatin jihar ta na kan bakarta cewa ba za su yi sulhu da ƴanbindiga ba. Amma ya ce a shirye gwamnatin jihar take ta karɓi duk wani ɗanbindigar da ya tuba da kansa, ya miƙa wuya. A ranar litinin ne…
Sojojin Nijeriya sun tabbatar da kashe wasu makusantan kasurgumin ɓarayin daji Bello Turji wanda suka addabi yankin Arewa maso yammacin Nijeriya. Sanarwar da daraktan yada labaran hedkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ta ce sumamen da sojin ƙasar suka kai Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da kuma Chindo sun yi sanadiyyar kashe gomman ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji da aka kashe a Fakai. “Ƙarfin wutar da sojojin suka buɗe ya janyo mutuwar ‘yan ta’adda da yawa tare da lalata cibiyar adana kayayyakinsu. Harin ya kuma yi sanadiyyar ‘yanta wasu mutane…
Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan korafe-korafen da al’umma suka shigar gabanta tare da wasu malamai a Jahar Kano kan Usaman Sojaboy dangane da wani sabon salon waka da yake kokarin fitowa da shi a wanda ya saba da koyarwar addinin musulunci tare da al’adar malam Bahaushe. A wata sanarwa da jami’in yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya aminche da kwace lasisin mawakin Sojaboy da Shamsiyya Muhammad tare da Hassana Suzan ya yin da sanarwa ta bukaci masu gidajen wasanni tare…
A karon fakro, shugaban rundunar RSF a Sudan ya amince da cewa dakarunsa sun yi rasa birnin Wad Madani ga rundunar sojin ƙasar da suke yaƙa, a wani koma-baya mafi girma da rundunarsa ta fuskanta tun bayan ɓarkewar yaƙin basasar ƙasar. A cikin wani sakon murya, an ji Janar Mohamed Hamdan Dagalo, na magana cikin fushi da takaici, yana lasar takobin ci gaba da yaƙi ko nan da zuwa shekara 20 ne. ”A yau mun yi rashin nasara a filin daga, amma ba mu yi nasara a wannan yaƙi ba, watanni 21 kenan muna yakar sojin Sudan, don haka za…
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun ce an yi jana’izar ‘yan aikin sa kai da wani jirgin yaƙi da ake zargin na sojojiin Najeriya ya kai musu hari bisa kuskure a ƙauyen Tungar Kara. Wani mazaunin ƙuyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana’aizar ‘yan sa kan su 17 da suka mutu a harin, yayin da wasu ke kwance a asibiti. A ranar Asabar da maraice ne wani jirgi da ake kyautata zaton na sojin ƙasar ne ya kai hari bisa kuskure kan ‘yan sa kai a ƙauyen na…
Real Madrid da Barcelona za su kara a wasan karshe a Spanish Super Cup a yau Lahadi a Saudi Arabia. Real Madrid ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta doke Mallorca 3-0 ranar Alhamis a filin wasa na King Abdallah a karawar daf da karshe ta biyu. Ita kuwa Barcelona ta kai wannan gurbin, saboda cin Athletic Club 2-0 da ta yi ranar Laraba a wasan daf da karshe na farko a dai Saudi Arabia. Wannan shi ne wasan farko na El Clasico a 2025, karo na huɗu a jere da za su fafata a Spanish Super Cup. Wannan…
Gwamnatin Jihar Kano dake arewacin Najeriya, ta bayyana matsayarta kan sabbin dokokin haraji da ake tattaunawa a Majalisar dokokin kasar. Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne lokacin bikin sabuwar shekarar 2025 da aka gudanar a Filin Mahaha da ke Ƙofar Naisa. Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, Gwarzo, ya ce “Waɗannan dokokin haraji ba su ne mafita ga matsalolin tattalin arziƙinmu ba”. Ya ƙara da cewa jihar Kano ba zata yarda da kowace doka da za ta cutar…
