Gwamnatin jihar Katsina dake Arewacin Najeriya ta musanta batun cewa ta fara shiga sasanci da ƴanbindigar jihar, inda ta ce ko kusa babu hannunta a ciki.
Gwmanatin ta bayyana hakan ne bayanda wasu jagororin ƴanbindiga suka miƙa bindigogi da mutanen da suka yi garkuwa da su ga sojoji a jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Katsina, Dr. Bala Salisu ya ce gwamnatin jihar ta na kan bakarta cewa ba za su yi sulhu da ƴanbindiga ba.
Amma ya ce a shirye gwamnatin jihar take ta karɓi duk wani ɗanbindigar da ya tuba da kansa, ya miƙa wuya.
A ranar litinin ne rundunar sojin Najeriya ta ruwaito bayyana cewa wasu manyan ƴanbindiga sun miƙa wuya ta hanyar mika bindigogi da mutanen da suka yi garkuwa da su ga sojoji a jihar ta Katsina.