Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Sojojin Nijeriya sun sanar da kashe ɗan Bello Turji
Afrika

Sojojin Nijeriya sun sanar da kashe ɗan Bello Turji

January 20, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Sojojin Nijeriya sun tabbatar da kashe wasu makusantan kasurgumin ɓarayin daji Bello Turji  wanda suka addabi yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.

Sanarwar da daraktan yada labaran hedkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ta ce sumamen da sojin ƙasar suka kai Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da kuma Chindo sun yi sanadiyyar kashe gomman ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji da aka kashe a Fakai.

“Ƙarfin wutar da sojojin suka buɗe ya janyo mutuwar ‘yan ta’adda da yawa tare da lalata cibiyar adana kayayyakinsu. Harin ya kuma yi sanadiyyar ‘yanta wasu mutane da Bello Turji ya yi garkuwa da su. Kuma shugaban ‘yan ta’addan, Bello Turji, ya tsere ya bar ɗansa da sauran mayaƙansa,” in ji sanarwar.

Bello Turji yana cikin ɓarayin daji da suka yi ƙaurin-suna wajen garkuwa da mutane da kisa a arewa maso yammacin Nijeriya.

Sai dai a ƙarshen shekarar da ta gabata dai hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta kashe Bello Turji.

Haka kuma a ƙarshen makon jiya ne rahotanni suka ce ɗan ta’addan yana tsere wa harin sojojin Nijeriya.

Kazalika sojin ƙasar sun lalata dabar wani ɗan ta’adda da ake kira Idi Malam a kan hanyar dajin Zango Kagara, in ji sanarwar.

“A lokacin arangamar, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da kama mutum uku da ake zargi da haɗa baki da su,” in ji Janar Buba.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.