Gwamnatin Jihar Kano dake arewacin Najeriya, ta bayyana matsayarta kan sabbin dokokin haraji da ake tattaunawa a Majalisar dokokin kasar.
Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne lokacin bikin sabuwar shekarar 2025 da aka gudanar a Filin Mahaha da ke Ƙofar Naisa.
Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, Gwarzo, ya ce “Waɗannan dokokin haraji ba su ne mafita ga matsalolin tattalin arziƙinmu ba”.
Ya ƙara da cewa jihar Kano ba zata yarda da kowace doka da za ta cutar da walwalar al’ummarta ba.
Haka kuma Kwamared Aminu ya yaba wa jajircewar al’ummar Kano wajen fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi, inda ya ce sam harajin bai dace ba.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi gwamnati ta fi mayar da hankali kan yaƙi da talauci da yunwa, musamman a yankin Arewa, wanda ke fama da tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Mataimakin Gwamnan, ya na mai jaddada nasarorin gwamnatin Kano a ɓangarorin lafiya, ilimi, samar da hanyoyi, da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje.