Hamas ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da Isra’ila domin tsara sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila take cigaba da kutsawa ƙasar, inda ta ce tana da burin ƙwace sassan Gaza ne. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce Isra’ila ta kashe sama da mutum 250 daga ranar Alhamis da ta gabata. Isra’ila na cigaba da luguden ne duk da matsin lamba da take fuskanta kan ta cire takunkumin mako goma da ta saka na hana shigar da kayan agaji Gaza, inda har Amurka ta nuna rashin jin daɗinta. Sannan Majalisar Ɗinkin Duniya…
Author: Wafsym
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata raba kujerun zama Fiye da Dubu goma sha shida a makarantun Firamare dan magance zaman Yara a kasa da Inganta harkokin kayo da koyarwa. Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar inda ake samar da ababan zaman daliban a Unguwar Gandun Albasa da yammacin Jiya Lahadi. Abba Kabir ya kara da cewar “samar da kujerun zaman dalibain da aka shafe watanni takwas ana hadasu ya samo asali ne daga Dokar ta baci da gwamnatinsa ta sa a fannin Ilimi don Ingantashi” Gwamna ya kuma ce “Gwamnati…
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba kabir yusif, ya ce gwamnatinsa zata samar da ruwansha a masarautar Rano da garuruwan dake karamar hukumar ta hangar samar da matatar suwa dutsen Taluwaiwai dake karamar hukumar. Gwamnan ya bayana hakan lokacin da ya Kai ziyarar aiki da yammacin yau Talata yana mai cewa “Yanzu haka gwamnati zata kawo kwararu dan yin bincike tare da samar da injinan yace ruwa na zamani” Cewar Gwamnan Kano. Gwamnan ya kuma umarci Ma’aikatar ruwa ta jihar Kano ta gagauta bin hanyoyin da za a kammala aikin cikin kankanin lokaci.
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) tare da Hukumar Hana Fataucin Mutane (NAPTIP) sun kafa wata rundunar jami’an su domin hada karfi tare wajen yaƙi da safarar miyagun kwayoyi da safarar mutane. Wannan mataki ya fito ne a lokacin da Shugabar NAPTIP, Binta Lami Adamu Bello, ta kai ziyarar girmamawa ga Shugaban NDLEA, na Kasa Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa, mai ritaya a hedikwatar NDLEA dake Abuja, yau jumma’a 25 ga Afrilu, 2025. A cikin jawabinsa, Marwa ya taya Binta Adamu Bello, murna bisa nadinta da shugaban Kasa Bola Ahamad Tunibu,yayi kuma ya yaba da yadda ta…
Mai Martaba Sarkin Hadeja kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maje, Ya ce kamata yayi Al’umma da kungiyoyi sun maida hankali wajen tallafawa masu ciwon koda dan ragemusu radadin halin da suke ciki sakamakon tsadar rayuwa. Sarkin ya bayyana hakand a safiyar Alhamis, lokacin da Gidauniyar dake talafawa masu ciwon koda ta Kidney Care Foundation ta mika talafin kayan wankin koda da kudin su ya Kai fiye da miliyan daya da rabi ga masarautar Hadeja dan ragewa masu lalurar tsadar rayuwa. Sakin na Hadeja ya kara da cewar masarautar hadeja na kan gaba wajen yawan masu ciwon…
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya Sanya Hannu Kan Dokoki Hudu da zasu Kafa Sabbin Hukumomi a Jihar . Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce sa hannu kan dokokin zai inganta ayyukan gwamnati da habaka ci gaban al’umma da tattalin arziki. Ta cikin waata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Alhamis, ta kara da cewar Hukumomin da aka kafa sun hada da Hukumar Kare Walwalar Jama’a ta Jihar Kano wato Kano State Social Protection Agency, Da Hukumar Kula da Tallace-Tallace na alluna ta Jihar Kano wato- Kano State Signed Advertisement Agency.…
Gwamnatin jihar Kano ta zata inganta tare da dawo da cibiyoyin koyar wa matasa dinki da tsohuwar Gwamnatin Dr Rabiu Musa Kwankwaso ta samar akayi watsi da su tsahon shekaru takwas a kananan hukumomin jihar dan samar da ayukanyi ga mata da matasa. Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayana hakan yayin ziyarar duba aikin titin kilomita biyar da da gyaran asibitin Minjibir da yammacin jiya Litinin. Gwamna Abba Kabir Yusif, ya kara da cewa ayukan suna cikin alkawaarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe kuma kyautata rayuwar matasa na cikin abubuwan da Gwamnatin sa ta bawa…
Majalisar karamar hukumar Minjibir a nan Kano zatayi dokar da zata hukunta, masu fadan Daba kilisa,da Kidan a fanin karamar hukumar sakamakon matsalolin da suke haifarwa. Shugaban karamar hukumar ta Minjibir Kaftin Jibrin Na lado Kunya,ne ya bayana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a karamar hukumar da Kungiyar Minjibir Solidarity Forum ta shirya dan kara kawo cigaba a karamar hukumar dama jihar Kano baki daya. Kaftin Jibrin Na lado Kunya Ya kara da cewar “yanzu haka majalisar karamar hukumar ta Minjibir ta kamala tataunawa da masu ruwa da tsaki musamman a fanin tsaro da zamantakewa dan samar…
Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja Nyesom Wike, yavce jam’iyyar PDP bata shirya karɓar mulki a hannun APC ba a kakar zaɓe ta shekarar 2027. A cewar Wike ko kaɗan babu wani cikakken tsarin da PDP ta yi wanda ke nuna cewa tana da shirin karɓar mulkin. Ministan ya bayyana hakan a yau juma’a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja. Nyesom Wike, dai ya na daga cikin manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya wanda har yanzu ke yin ikirarin cewa shi ɗan jam’iyyar PDP ne, tare da shan alwashin yin duk mai yiwuwa wajen kayar da ita a zabe…
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano dake arewacin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Darakta Alhaji Sani Anas, ta ce ta shawo kan wata gobara da ta tashi a kasuwar kurmi tare da kone shaguna shida a layin masu sayar da wayoyin hannu wato yan Jjagwal. Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar ga manema labarai ta kara da cewa hukumar kashe gobarar ta karɓi kiran gaggawa daga DPO na ofishin ‘yan sanda na Jakara a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 1:35 na dare, game da gobara da ta tashi a kasuwar Kurmi,…
