Mai Martaba Sarkin Hadeja kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maje,
Ya ce kamata yayi Al’umma da kungiyoyi sun maida hankali wajen tallafawa masu ciwon koda dan ragemusu radadin halin da suke ciki sakamakon tsadar rayuwa.
Sarkin ya bayyana hakand a safiyar Alhamis, lokacin da Gidauniyar dake talafawa masu ciwon koda ta Kidney Care Foundation ta mika talafin kayan wankin koda da kudin su ya Kai fiye da miliyan daya da rabi ga masarautar Hadeja dan ragewa masu lalurar tsadar rayuwa.
Sakin na Hadeja ya kara da cewar masarautar hadeja na kan gaba wajen yawan masu ciwon kodar dan haka tallafin zai taimaka wajen saukakawa masu fama da cutar kodar.
Da yake jawabi tun da fari Shugaban Gidauniyar Ibrahim Haruna, wanda Farfesa Aliyu Abdu, ya wakilta cewa yayi Gidauniyar na tallafawa masu fama da ciwon koda na kashe kudi mai yawa wajen wankin jini shiyasa suke samar da tallafin,
A nasa jawabin shugaban Asibitin Hadeja, Wanda Director Clinical Service Abba Ali ya wakilta, cewa yayi Asibitin zai yi amfani da kayan yadda ya kamata dan tallafawa masu ciwon kodar.
Gidauniyar ta Kidney Care Foundation ta ce zata cigaba da tallafawa mutanen da za a yiwa dashen koda wajen biya musu wani kaso na kudin da za a yi musu aikin.