Majalisar karamar hukumar Minjibir a nan Kano zatayi dokar da zata hukunta, masu fadan Daba kilisa,da Kidan a fanin karamar hukumar sakamakon matsalolin da suke haifarwa.
Shugaban karamar hukumar ta Minjibir Kaftin Jibrin Na lado Kunya,ne ya bayana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a karamar hukumar da Kungiyar Minjibir Solidarity Forum ta shirya dan kara kawo cigaba a karamar hukumar dama jihar Kano baki daya.
Kaftin Jibrin Na lado Kunya Ya kara da cewar “yanzu haka majalisar karamar hukumar ta Minjibir ta kamala tataunawa da masu ruwa da tsaki musamman a fanin tsaro da zamantakewa dan samar da dokar Wanda zatayi tanadi kan irin hukuncin da masu fadan Daba, Kidan Dije da kuma masu kilisa zasu fuskanta matukar suka sabawa dokar”shugaban karamar hukumar Minjibir.
A nasa jawabin Tun da fari tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano kuma mataimakin shugaban kungiyar ta kasa Kwamared Kabiru Ado Minjibir cewa yayi “Sai an samar dokar da zata sahalewa duk Wanda zai yi Kilisa ko kidan Dije dan samar da mafita ga abubuwan dake biyo baya na fadan Daba Tsakanin matasan karamar hukumar domin bai kamata a zubawa lamarin idanu yana jawo asarar dukiya da jikkata Al’umma ba Amma samar dokar da tsarin da masu kilisa ko kidan DJ zasu bi bayan Neman izzini zai sa Wanda suka shirya irin wannan taruka su tabbatar da ganin cewa ba a samu karya doka ko cin zarafin mutane ba”Cewar Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Kasa Kabiru Ado Minjibir.
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar ta Minjibir Solderity Forum, ya ce “Makkasudin taron shi ne samar da hadinkai da kuma kawo Ayukan cigaba karamar hukumar Kamar Hanyoyi, Samarwa matasa ayukan yi da kuma Ilimin sai ababen more rayuwa.
Wakilinmu ya rawaito cewa taron ya samu halartar mutane yan asalin karamar hukumar ta Minjibir da sukayi fice a fanin siyasa,aikin Gwamnatin da kasuwanci da kuma masu bawa karamar hukumar gudunmawar da ta kama a fanin da suke da kwarewa.