Hamas ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da Isra’ila domin tsara sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila take cigaba da kutsawa ƙasar, inda ta ce tana da burin ƙwace sassan Gaza ne.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce Isra’ila ta kashe sama da mutum 250 daga ranar Alhamis da ta gabata.
Isra’ila na cigaba da luguden ne duk da matsin lamba da take fuskanta kan ta cire takunkumin mako goma da ta saka na hana shigar da kayan agaji Gaza, inda har Amurka ta nuna rashin jin daɗinta. Sannan Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce hanin a daidai lokacin da ake cigaba da ɓarin wuta yunƙurin kisan ƙare dangi ne.