Author: Wafsym

Mai martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammadu Sunusi Na Biyu,ya ce Sai Iyaye da sauran Alumma sun Koma bin koyarwar Addini da kuma Inganta tarbiya matukar ana son fita daga halin gubacewar marasa da ake fuskanta fadin jihar Kano da Kasa Baki daya. Sarkin ya bayana hakan lokacin saukar karatun Alkur’ani Mai girma na dalibai Saba’in Karo na takwas da ya gudana Jiya Lahadi a makarantar Ma’ahad Abdulhamid littahfezil Kur’an dake Unguwar Shatsari cikin karamar hukumar dala a nan Kano. Mai martaba Sarkin na Kano Wanda Jarman Kano Alhaji Ahmad Umar, ya wakilta ya Kara da cewar Kula da tarbiya da…

Read More

Ma’aikatar mata da Kananan Yara da kuma masu bukata ta musamman taci alwashin hada hannu da ma’aikatar Ilimi ta jihar dan kawo karshen cin zarafin kananan yara a makarantu. Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata Hajiya Amina Adullahi Sani HOD, da ta samu wakilicin Daraktan Mulki da gudanarwa na ma’aikatar, Muhammad Sambo Iliyasu, ce ta bayyana hakan yayin bikin ranar yara ta Duniya da ya gudana a dakin taro na gidan gwamnatin Kano a jiya Talata. Itama shugabar gudauniyar EL’S Foundation tace zasu dauki nauyin wasu daga cikin yaran da suka nuna kwazo a wajen taron dan tallafa musu. Wakilinmu SSM ya rawaito…

Read More

Karamar hukumar Rano ta bukaci al’ummar garin da su kwantar da hankalin su tare da bin Doka da oda Inda zata ci gaba da bin kadin hatsaniyar da ta faru a baya bayan nan da ya haddasa rasuwar Baturen ‘yan sandan Yankin wato DPO, da wani matashi Bakanike. Shugaban karamar hukumar Hon Muhammad Nazir Ya’u ,ne ya bukaci hakan a yammacin yau a wani taron manema Labarai da ya gudana a sakatariyar ‘yan Jaridu ta jiha NUJ. Muhammad Naziru Ya’u , ya ce karamar hukumar na aiki tare da Jami’an tsaro da masu Ruwa da Tsaki a Fannonin Rayuwa daban…

Read More

Gwamnatin jihar kano ta ce ya kamata iyaye su dunga sanya idanu akan ƴaƴan su mata wajen sauke duk wani nauyi da yake kan su musamman yadda ƴaƴa mata suke da rauni da kuma wasu buƙatu da suke da su amma basa iya bayyanawa. Babbar Daraktan Bincike da Adana bayanai ta gidan gwamnatin kano Hajiya Nana Asma’u Jibrin ce ta bayyana hakan a yau cikin wani ɓangare na ranar Al’adar mata ta duniya yayin bayar da tallafin kayan anfanin mata na yau da kullum ga ɗaliban makarantar First Lady dake nan kano domin ragewa iyaye nauyin siya musu. Nana Asma’u…

Read More

Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan dari da hamsin da Daya don sake gina masallacin da wani matashi ya kona masallata a garin Tiga  Gadan dake karamar hukumar Gezawa a ranar 16 ga watan Mayun shekarar data gabata ta 2024. Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da alamuran cikin gida na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar. Sanarwar ta kuma ce,  ginin zai hadar da na Islamiyya da Ofisoshi da kuma  gyaran bandakuna tare da samar da wutar Sola da kuma fanfan tuka-tuka. Gyaran masallacin na daga cikin…

Read More

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da aukuwar wani mummunan lamari a ranar 25 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 8:15 na dare a karamar hukumar Rano, inda aka kama wani mai gyaran babur mai suna Abdullahi Musa, ɗan asalin Rano, bisa zargin tuƙin babur cikin haɗari da kuma yiwuwar kasancewa cikin maye, bayan korafe-korafe daga jama’a. Bayan an tsare shi, sai ya fara nuna alamun rauni, wanda ya sa aka garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Rano, inda ya rasu a safiyar ranar 26 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 6:00 na safe yayin da ake kula…

Read More

Babbar kotun shariar musulunci ta Rijiyar zaki wadda ke zamanta a Danbare ta yankewa matashin nan wato Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe wasu mutane yayin da suke gudanar da sallar Asuba a garin gadan dake karamar hukumar Gezawa. Lauyan gwamnati Barista Salisu Muhammad Tahir ya gabatar da lauyoyin dake mara masa baya wato Barista Yusura M Hanga da Barista Basiru Aliyu Itama lauya mai kare wanda ake tuhuma daga ofishin lauyoyin taimako Barista Asiya Imam ta gabatar da kanta. Mai sharia Halhalatul Kuzai Zakariyya yayi karatun baya yakuma sake karanto tuhume tuhumen kisan…

Read More

A wani salo na tabbatar da doka tare da kawo tsafta a bangaren Dab’i, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh. Abba El-mustapha ta kara yin nasarar ganowa tare da kama wasu na’urori da ake amfani dasu wajan buga hotunan batsa ga masu sana’ar maganin Gargajiya a cikin wasu unguwannin Jahar Kano wanda suka hada da komfutoci da Kuma injinan buga hotuna wato (Printers). Da yake holan kayan da Hukumar ta kama Alh. Abubakar Zakari Garun Babba darakan Dab’i na hukumar ya bayyana guraren da aka kama wannan kaya sun hada da wasu unguwani a karamar…

Read More

Gamayyar kungiyar tsaffin daliban makarantan Abdullahi Mai masallacin dake Unguwar Gini cikin karamar hukumar Birnin Kano ta ce zata cigaba da samar da kayan koyo da koyarwa dan tallafawa dalibai masu tasowa da Bunkasa Ilimi. Shugaban kungiyar Nura Yusif,ne ya bayana haka jiya Lahadi lokacin da yake kadamar da dakin gwaje-gwajen da kungiyar ta daga darajarsa tare da samar da kayan aiki na zamani a makarantar Abdullahi Mai Masallaci dake Unguwar Gini a nan Kano. Nura Yusif, ya Kuma Kara da cewar sun tara kudaden da suka tallafawa makarantar ne daga mambobinsu da Kuma daidaikun mutanen tare da kashe fiye…

Read More

Babbar Kotun Tarayya me lamba 1 dake Gyadi gyadi Court Road Karkashin me Shari’a SM Shu’aibu ta yi umarni ga Hukumar EFCC data cigaba da bincike kan filin Musabaka da ake zargin wasu Jagororin Musabaka a Jihar Kano sun siyar ba bisa ka’ida ba Asali dai tsohon Gwamnan Jihar Kano Marigayi Abdullahi Wase ne ya bayar da filin ga ‘Yan Musabaka a shekarar 1995 a yankin Ahmad Bello dake Nassarawa GRA dan gina Cibiyar Musabaka, hakan yasa wasu daga cikin masu musabakar su kayi korafi a gaban hukumar EFCC data yi bincike kan lamarin, haka tasa ‘Yan Kwamitin suka garzaya…

Read More