Kungiyoyi masu zaman kansu da ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana damuwarsu kan yadda cutar hawan jini ke yaduwa a Nijeriya, inda suka ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin rage haɗarin da cutar ke haifarwa. Shugaban wata ƙungiya mai lura da lafiyar jama’a ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da suka gudanar shi ne samar da takardar bayanai kan cututtukan da ke kama zuciya wacce gwamnati za ta iya amfani da ita wajen tsara manufofi. Ƙungiyar ta haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen horar da ma’aikatan jinya kan yadda za su kula da masu fama da hawan jini…
Author: Wafsym
A makon da ya gabata, wasu jihohi biyu da babban birnin tarayya, Abuja, sun fuskanci barkewar cututtuka daban-daban, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma da hukumomin lafiya a Nijeriya. Adamawa: Cutar Kuraje Ta Buruli Ulcer Ta Kashe Mutum Bakwai Jihar Adamawa ta samu barkewar cuta mai zagwanye naman jiki, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cutar a matsayin Buruli Ulcer, wadda ake samun ta a karkara musamman wuraren da ke kusa da ruwa. Dr. Adesigbin Olufemi na shirin kasa na dakile cutar tarin fuka da kuturta a Nijeriya ya…
Allah Ya yiwa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari rasuwa a yau ranar Lahadi yana da shekara 82 da haihuwa. Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar ta ce Buhari ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan. Fadar shugaban Najeriya ta ce ya rasu da misalin ƙarfe 4:30 “sakamakon doguwar jinya”. A wani labarin kuma, shugaba Ahmed Tinubu ya umarci Mataimakin sa Kashim Shettima da ya tafi Landan domin ya rako gawar Buhari zuwa gida Najeriya,, inda ake sa ran yi masa jana’iza a mahaifarsa watau garin Daura a jihar Katsina. Allah Ya jikansa amin
Kwalejin Ilimi ta Isa Kait dake Karamar Hukumar Dutsenma a Jihar Katsina zata rika shiya taron bita dan tunawa da Gudunmawar da wazirin katsina Marigayi Isa Kaita ya bayar dan tunatar da matasa muhimancin sadaukar da lokacin su wajen bunkasa rayuwar Al’umma da cigaban Kasa. Shugaban kwalejin Dakta Ismaila Ado Funtuwa ne ya bayyana hakan yayin taron tunawa da gudunmawar da Marigayi Isa Kaita ya bayar lokacin yana raye karo na farko yau Laraba a kwalejin ta Isa Kaita College of Education dake karamar Hukumar Dutsenma a Jihar Katsina. Ismaila Ado Funtuwa ya kuma CE gudun mawar da Marigayi Isa…
Gwamnatin jihar kano ta umarci masu gudanar da sana’ar gwangwan dake jihar kano da su dakatar da sayo kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas na ƙasar nan sakamakon iftila’in da aka samu a jihar nan a kwanan nan kan yadda aka samu abubuwan fashewa a jihar sanadiyyar kayan gwangwan da suke da alaƙa da yankin Arewa maso gabas ɗin ƙasar nan. Kwamishinan tsaro na jihar kano AVM Ibrahim Umaru mai ritaya ne ya bayyana hakan a yau yayin wata ganawa da ƙungiyar masu sana’ar gwangwan na ƙasa reshen Arewa kan irin iftila’in da ya fara a jihar Kano a…
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I Jibrin ya ce da zarar shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya mika masa gayyatar zama mataimakinsa a zaben shekarar 2027 da gudu zai karɓa. Barau wanda ke ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin gudanar da duk wani aikin da shugaban ƙasar ya ba shi. Sanatan wanda ya bayyana cewar ba ya buƙatar yin dogon jawabi dangane da lamarin a halin yanzu, ya ce lokaci bai yi ba da jama’a za su dinga tallata shi domin zama mataimakin shugaban ƙasa a zabe mai…
Masana a fanin dokokin Tuki na cigaba da bayana takaicin su kan yawan karya dokar amfani da sigina ta alamar shiga kwana ko danjar dake nuna alamun tsayawa da masu ababen hawa ke kin amfani dasu hakan kuma ke jawo asarar dukiya da rayuka sakamakon haifar da hatsari. A zantawarmu da wasu dake tafiya a babur mai Kada biyu sun bayana cewa da yawan cikin masu mota ko baburin adaidaita sahu na tsayawa ko shan kwana batare da saka alama ba walau danja birki ko sigina Wanda suka ce hakan na jawo hadura kamar Yadda suka Bayana. Sai dai wasu…
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya dawo gida Najeriya a yamacin yau Laraba Inda ya sauka a filing jirgin Sama na Malam Aminu Kano Bayan gudanar da Ibadar aikin Hajji shekarar 2025. Abba Kabir Yusif ya dai shafe mako biyu a Kasa Mai tsarkindanbgudanar da aikin hajin Yayin da ya kasance Amirul Haji na Jihar Kano. Haka kuma Gwamnan ya samu tarba daga manya jami’an Gwamnatin Kano ,shugabanin kananan hukumomin da masu bashi shawara da sauran magoya baya da suka fito daga sasan Jihar Daban-daban.
Yayin da ake shirin gudanar da ranar Dimokaradiyya a kasar nan a gobe Alhamis 12 ga watan Yuni, wasu rukunin mutane sun shirya gudanar da zanga-zanga a jihohi 20 na kasar nan. Cikin wata sanarwa da suka fitar a yau talata, sun ce za a gudanar da zanga-zangar ne sakamakon wahalar rayuwa da rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi tare da tabarbarewar al’amura. Ko’odinetan tattakin na kasa, Juwon Sanyaolu, yace zasu gudanar da tattakin ne a jihohi 20 na kasar nan. Wasu daga cikin jihohin da zanga-zangar zata gudana sun hadar da Abuja da Edo da Niger…
Hukumar kiyaye hadura ta kasa zata gudanar da bincike Kan musabbabin faruwar hadarin da yayi sanadiyar mutuwar mutanen ashirin da Biyu a nan Kano wanda suka wakilci jihar a bikin wasanni na Kasa da aka gudanar Ogun. Shugaban hukumar na Kasa Shehu Muhammad,ne ya bayana hakan lokacin da tawagar hukumar kiyaye haduran suka kawo ziyartar ta’aziya gidan gwamnatin Kano a jiya litinin. Shugaban hukumar kiyaye haduran ta kasa Wanda mukadashinsa Mai Lura da shiya ta daya dake jihar Kaduna Ahmad Umar,ya wakilta,ya kara da cewar yanzu Haka hukumar ta fara bincike musabbabin yaawan faruwar hatsari a gadar ta Yan kifi…
