Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta fara aiwatar da cikakken haramcin ɗaukar fasinja a kan babura, tare da takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a wasu kananan hukumomi. Dokar, wacce gwamnatin jihar ta kafa a baya, tana shafar Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (yanki na Jido) da Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya da Jido Ward). Kano: Duk Wanda Aka Kama Yana Achaba Za A Kwace Masa Babur Tare Dadaurin Watanni 6 Da Tara — Kwamishinan Shari’a Kwamishinan ‘Yansandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi masu babura da adaidaita sahu da…
Author: Wafsym
Gwamnatin Jihar Kano ta sake tunatar da jama’a cewa duk mai aikin ɗaukar fasinja da babur (Achaba) a wasu yankuna na birnin zai fuskanci hukuncin daurin watanni 6, tara N10,000 ko duk biyun, tare da kwace babur, idan aka kama yana karya doka. Abdulkarim Kabiru Maude, SAN Babban Lauya Gwamnati, Kuma Kwamishinan Sharia Na Jihar Kano ne ya bayyana hakan ga manema labarai Datti Baba-Ahmed ya ce ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro “bai da amfani” ”Ya ce dokar hana Achaba ta shafi Kananan Hukumomin: Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo, Dawakin Kudu, Fagge, da Kumbotso.” Ga sauran Kananan Hukumomin…
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya soki matakin Shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a faɗin ƙasar, yana mai cewa matakin “bai dace ba, kuma ba shi ke magance matsalar tsaro ba.” A hirar da ya yi da Arise TV, Baba-Ahmed ya ce dokar ta-ɓacin “ta samo asali ne daga rashin fahimtar ainihin matsalar da ake fuskanta,” yana mai kiran matakin “abin ban dariya da ba zai kawo canji ba.” Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya Ya kuma soki shawarar gwamnatin tarayya ta…
Bankin Duniya ya yi gargadi cewa karuwar yawan jama’a a Nijeriya na iya haifar da karin matsaloli musamman a fannin tsaro da tattalin arziki. Rahoton bankin ya nuna cewa idan ba a dauki matakan da suka dace ba wajen samar da ayyukan yi, inganta ilimi da walwalar jama’a, to kasar na iya fuskantar karin rikice-rikice da rashin zaman lafiya a nan gaba. Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki Bankin ya kuma jaddada bukatar gwamnati ta zuba jari sosai wajen bunkasa noma, kiwon lafiya da ilimi domin rage tasirin karuwar jama’a ga tsaron kasa da…
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda ba’a bayyana sunan sa ba, na fuskantar bincike kan zargin cewa yana da alaƙa da wasu jami’an soja da ake tsare da su bisa zargin shirin juyin mulki. Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa ana zargin tsohon gwamnan da taimaka wa da kuɗi wajen shirya juyin mulkin da aka ce an tsara shi a gudanar ranar 25 ga Oktoba. Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani Rahotanni daga wasu kafafen labarai sun ce jami’an da ake tsare da…
Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Jihar Kano (KIRS) ta kaddamar da wani sabon tsari na zamani da nufin sauya yadda al’umma ke biyan haraji a fadin jihar, tare da tabbatar da inganci, gaskiya da sauƙi a tsarin tattara kudade. Sabon tsarin, wanda ya fito ne a ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na ƙara yawan kudaden shiga na cikin gida da rage dogaro da tallafin gwamnatin tarayya, ya mai da hankali kan amfani da fasahar zamani da haɗa bayanan masu biyan haraji da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN). Wannan, a cewar hukumar, zai taimaka wajen gano masu kauce wa…
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk wanda ke son tsayawa takara ko samun mukamin siyasa a Najeriya, abin da ake buƙata kawai shi ne takardar shaidar kammala makarantar sakandare. Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda ya ce tsarin doka a Najeriya bai tilasta sai mutum yana da manyan takardun karatu kafin shiga siyasa ba. NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya A cewarsa, “Doka ta bayyana a fili cewa takardar shaidar sakandare ta isa mutum ya tsaya takara ko ya…
Aƙalla, mutane 4,778 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar kwalara a Najeriya, tsakanin shekarar 2020 and 2024, a cewar hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a ƙasar(NCDC). Alƙaluman hukumar sun nuna cewa a shekarar 2020, mutum 3,513 ka yi zaton sun kamu da cutar, kuma a cikinsu mutum 95 sun mutu. Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi kan kudi N70,000 ta sanya a zukatan yan Nijeriya Sai dai alƙaluman sun ƙaru matuƙa a shekarar 2021, inda aka yi zaton mutane 111,062 suka kamu da cutar, kuma 3,604 suka mutu a jihohi 33 na ƙasar. A shekarar 2025 kaɗai…
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta kama wasu manyan masu safarar ƙwayoyi dake da hannu a shirin fitar da ɗaurin ƙwaya guda 6 daga ƙasar zuwa Ingila. Hukumar ta samu wannan nasara ne bayan aikin da ta shafe makonni 3 tana gudanarwa a jihar Lagos, wanda ya kai ga kame mutane 6, ciki har da shugabansu Alhaji Hammed Ode. Jami’in Ɗan Sanda Ya Harbe Kansa Da Bindiga Bisa Kuskure A Kano Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a Lahadin nan. Babafemi ya…
Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi malamai daga wajen jihar da kasa Baki daya da su daina yin magana ko sharhi da zai iya kawo cikas ga binciken da kwamitin shura ke gudanarwa kan zargin da ake yi wa Malam Lawan Abubakar Shu’aibu Triumph. Rahotanni na Bayyana cewa, sakataren kwamitin, wanda kuma shi ne Kwamishinan Kasuwanci na jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a Kano. Za’a yada zaman da zai gudana tsakanin majalisar Shura da Sheikh Lawan Triumph kai tsaye Sagagi ya ce gwamnati ta lura da yadda wasu malamai daga…
