A wani yanayi da ba a saba gani ba, an shiga watan Janairu na sabuwar shekara, amma har yanzu yanayin sanyi bai tsananta ba a wasu sassan ƙasar, musamman a yankunan arewacin Najeriya. A al’ada, watannin Disamba da Janairu sukan kasance lokacin sanyi mai tsanani, inda ake samun hazo mai kauri a wasu birane da ƙauyuka na Arewa. Sai dai a wannan karo, al’amarin ya sauya, lamarin da ya jawo damuwa da tambayoyi daga ɓangarori daban-daban na al’umma. Yadda dawowar sanyi ya sauya al’amura a Kano Yayin da wasu ke ganin sauyin yanayi ne kawai da ba shi da wata…
Author: Wafsym
Bayan shafe wasu makonni ana fama da zafi mai tsanani, birnin Kano ya sake fuskantar yanayin sanyi mai ƙarfi tare da ƙura da hazo, abin da ke nuna shigowar lokacin hunturu. Sauyin yanayin ya fara ne a ƙarshen makon da ya gabata, inda mutane da dama suka fara jin tasirinsa a rayuwarsu ta yau da kullum. Wasu mazauna birnin na cewa irin wannan yanayi na nuna yadda sauyin yanayi ke ƙara bayyana a Arewa cikin ‘yan shekarun nan. Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Kuɗin 2026 Na Naira Tiriliyan 4.4 Wakilinmu ya tattauna da wasu mazauna Kano domin jin…
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 4.4, bayan shafe lokaci tana gudanar da tattaunawa mai zurfi da nazari kan abubuwan da ke cikinsa. Majalisar ta bayyana cewa ta amince da kasafin ne domin ganin yadda zai taimaka wajen bunƙasa rayuwar al’ummar jihar, musamman ta fuskar samar da ababen more rayuwa, inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, da kuma haɓaka tattalin arziki. Yan siyasan Arewa da malaman addinin Arewa da sarakunan Arewa su ne suka sayar da Arewa —Naja’atu Muhammad Shugaban Majalisar, Mudashiru Obasa, ya ce ‘yan majalisar sun tabbatar…
Fitacciyar ’yar gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Naja’atu Muhammad, ta zargi wasu ’yan siyasa, malaman addini da kuma sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya da cewa su ne suka gaza kare muradun yankin, lamarin da ta ce ya janyo koma-baya da tarin matsaloli a Arewa. Naja’atu ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da DCL Hausa, inda ta yi tsokaci kan makomar Arewacin Najeriya a siyasar 2027. Kotu ta tura Abubakar Malami da iyalansa gidan yarin Kuje A cewarta, duk da yawan jama’a da albarkatun da yankin ke da su, rashin jagoranci nagari daga masu ruwa da tsaki…
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), a Gidan Gyaran Hali na Kuje, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar belin sa. Alkalin kotun Mai Shari’a Emeka Nwite, ya kuma umarci a tsare ɗan, Abubakar Malami, da kuma daya daga cikin matan sa, Bashir Asabe, wadanda suke fuskantar shari’a tare da shi. Siyasar Kano: Shin Kwankwaso Ne Zai Tura Gwamna Abba Jam’iyyar APC ko Kuwa Gaban Kansa Yake Son Yi? Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan sauraron muhawara daga bangaren lauyoyin kare wadanda ake tuhuma,…
Siyasar Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ɗauki ɗumi sakamakon wasu bayanai da suka nuna cewa kowane lokaci daga yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf zai iya sauya sheka daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya. Waɗannan rahotanni sun yi karfi ne a ƙarshen makon da ya gabata bayan wasu jiga-jigan ‘yansiyasa da makusantan gwamnan sun fito fili inda suka yi ta kiraye-kiraye a gare shi, da kuma uban gidansa na siyasa Rabiu Musa Kwankwaso cewa ya kamata su ja su zuwa Jam’iyyar ta APC. Sheikh gumi ya soki farmakin saman Amurka a Najeriya Masu yin wannan kiran…
Shehin malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki farmakin saman da Amurka ta kai kan sansanonin ’yan ta’adda a Arewa maso Yammacin Najeriya, yana cewa hakan na iya ƙara rarraba al’umma tare da tauye ikon ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa sojojin Amurka sun kai hare-hare masu tsanani, yayin da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da haɗin gwiwar tsaro da musayar bayanan sirri da Amurka. ’Yan majalisar dokokin Kano 2 sun rasu Jaridar Punch ta ruwaito wani rubutu da ya wallafa a Facebook, ya nemi gwamnati ta dakatar da haɗin gwiwar soji da…
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta shiga jimami bayan rasuwar mambobinta guda biyu a ranar Laraba. Hon. Aminu Saad Ungogo, wanda ke wakiltar Ƙaramar Ungogo, shi ne mutum na farko da ya rasu a ranar Laraba. Jinkirin aiwatar da dokokin haraji zai cutar da ma’aikata da talakawa — shugaban kwamitin fadar shugaban ƙasa Labarin rasuwarsa, na cikin wani saƙo da hadimin gwamnan Kano, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook. Aminu Saad Ungogo “Allah Ya gafarta wa Hon. Aminu Saad Ungogo, ɗan Majalisar Jihar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar a Jihar Kano,” in ji Adam. Sa’o’i ƙadan, aka sake samun…
Shugaban Kwamitin fadar shugaban kasa kan Sauye-sauyen Haraji, Taiwo Oyedele, ya gargaɗi cewa jinkirta aiwatar da sabbin dokokin haraji bayan 1 ga Janairu, 2026, zai ƙara nauyin haraji ga ma’aikata da ’yan kasuwa a Najeriya. Oyedele ya ce kashi 98 cikin 100 na ma’aikata za su ci gaba da fuskantar haraji iri-iri, yayin da ’yan kasuwa za su rasa rangwamen da sabbin dokokin suka tanada. Ya bayyana haka ne a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels . An Kama ‘Yan Mata Biyu da Laifin Yunkurin Shigar da Miyagun Kwayoyi Cikin Gidan Yari a Kano Gargaɗin nasa na…
Hukumar kula da gyaran hali ta najeriya (NCOS) reshen jihar Kano ta kama ‘yan mata biyu bisa zargin ƙoƙarin shigar da abin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne cikin gidan gyaran hali da ke goron dutse. An kama su ne a ranar 21 ga Disamba, 2025, yayin binciken tsaro na yau da kullum a wajen shiga gidan yarin, inda jami’an tsaro suka cafke su suna ƙoƙarin samun izinin shiga. Wadanda aka kama su ne Maryam Ali da Hauwa Musa, mata ‘yan shekaru tsakanin 19 zuwa 20, mazaunan Kano, kuma an same su da wasu abubuwan da ake zargin ƙwayoyi ne…
