Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar alhini kan rasuwar aƙalla mutane 30 da suka mutu sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Kwanar Barde dake ƙaramar hukumar Gezawa. Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi. Gwamnatin Kano Ta Nemi Haɗin Kan ’Yan Kasuwa Don Rage Tsadar Kayayyaki A Ramadan Ya bayyana hatsarin a matsayin abin tausayi da babban rashi ba ga iyalan mamatan kaɗai ba, har ma ga daukacin al’ummar Jihar Kano. Rahotanni sun…
Author: Wafsym
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gana da shugabannin manyan kasuwannin jihar, domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen rage tsadar kayan masarufi a yayin watan azumin Ramadan. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Kwamared Sa’idu Yahaya, inda aka haɗa shugabannin kasuwannin Singer, Sabon Gari, Na’ibawa ’Yan Lemo, Dawanau, da Kasuwar Turawa ta ’Yan Kaba. “Shugabanci Amana Ne, Ba Tara Dukiya Ba” — Dr Getso Ya Yi Kira Ga Masu Nagarta Su Shiga Siyasa Da yake jawabi a wajen taron, Kwamared Sa’idu Yahaya ya ce an kira ganawar ne…
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Abdullahi Muhammad Getso, ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu tarbiyya da nagarta da su fito su shiga harkokin siyasa, domin gyara shugabanci a ƙasar. Dr Getso ya yi wannan kira ne yayin hudubar Juma’a a Masallacin Jami’ur Rahman Jumaat da ke Kundila, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane nagari da masu cancanta ke gujewa shiga takara, lamarin da ke barin siyasa a hannun masu son zuciya da rashin kishin kasa. Caca na Ci Gaba da Shafar Matasan Arewa, Hisbah Ta Yi Gargadi “Hakkin al’umma ne su gano shugabanni nagari, su ƙarfafa musu gwiwa…
Caca na ƙara yaɗuwa a tsakanin matasan Arewacin Nijeriya duk da haramci da gargadin addini, lamarin da ke jefa matasa cikin talauci da matsalolin rayuwa. A da, ana gudanar da caca ne a fili ta hanyar katin wasa, inda galibi matasa da marasa aikin yi ke taruwa. Sai dai a wannan zamani na fasahar intanet, wayoyin hannu sun ba masu caca damar gudanar da harkarsu a ɓoye, ba tare da sanin iyaye ko al’umma ba. Kotun Bauchi ta yanke wa barawon babur hukuncin kisa ta hanyar rataya Masana sun danganta wannan yanayi da tsananin talauci, rashin aikin yi, da yawaitar…
Akalla jami’an rundunar ’yansandan Nijeriya 5,000 ake sa ran za su yi ritaya a shekarar 2026, in ji Mataimakin Kwamishinan ’Yansanda mai kula da fansho a shalƙwatar NPF, DCP Sani Doki Yusuf. Yusuf ya bayyana hakan ne a Kano yayin taron horaswa na yankin Arewa maso Yamma ga jami’an da ke shirin ritaya, wanda NPF Pensions Limited ta shirya. Ya ce taron na da nufin wayar da kai kan muhimmancin cika takardun fansho yadda ya kamata domin kauce wa jinkiri wajen biyan haƙƙoƙi. Jami’an Ƴansanda 5,000 Ake Sa Ran Za Su Yi Ritaya A Shekarar 2026 Ya ce matsalolin da…
Babban Kotun Jihar Bauchi mai lamba hudu, ta yanke wa wani mutum mai suna Mamuda Zakariyau hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin kashe wani mai babur da wuƙa a lokacin da ya yi yunƙurin satar babur ɗin. Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Aliyu Baba Usman, ya ce: “Saboda kotu ta same ka da aikata laifin kisan kai, wanda hukuncinsa kisa ne, an yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya.” Kotu ta bayar da belin mutanen da suka bayar da shedar kanzon Kurege kan kisan Dorayi Lauyoyin Ma’aikatar Shari’a sun gabatar da tuhuma guda biyu a kan…
Kotun majistire mai lamba biyu da ke Nomans Land a Kano ta bayar da belin Abubakar Ali da aka fi sani da Bala da Munir Yahaya Dorayi. A zaman kotun na yau, an bayar da belin Munir Dorayi a hannun mahaifinsa, tare da sharadin cewa mai unguwa ko dagaci ko kuma babban limamin Dorayi zai tsaya masa, inda aka tanadi biyan tarar Naira dubu dari biyar idan ya tsere. Adana Tarihi Da Al’ada: Shugaban Hukumar Tarihi Na Kano, Arc. Ahmad Zai Karbi Kyautar Kasa Kwanan Nan Haka kuma, an bayar da belin Abubakar Ali wato Bala Dorayi, tare da sharadin…
DAGA SALISU MAISAJE Manajan Daraktan Hukumar Tarihi Da Al’adu Ta Jihar Kano, Arc. Ahmad Abba Yusuf na sahun gaba kan sunayen da a ke bincike a kan su dan ba da lambar girmamawa kan hobbasa wajen raya al’adu da kuma alkinta tarihin al’umma. Hadaddiyar kungiyar kungiyoyin dake nazari kan tarihi da al’adu na yammacin Afirka, dake da ofis a jihar Edo, ta shirya tsaf dan bayyana sakamakon wadanda su ka yi fice kan kudurorin da a ka yi nazari a kansu a shekarar da ta wuce ta 2025, na irin wadannan hukumomi. Najeriya: Fiye da rabin mata masu juna…
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kusan kashi 58 cikin 100 na mata masu juna biyu a Najeriya na fama da matsalar ƙarancin jini, sakamakon rashin cin abinci mai wadataccen sinadaran gina jiki. Shugabar sashen kimiyyar gina jiki a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Helen Achimugu, ce ta bayyana hakan ranar Talata a Abuja, yayin wani taron horas da manema labarai da ƙungiyar Civil Society–Scaling Up Nutrition in Nigeria (CS-SUNN) ta shirya. Taron, wanda ya mayar da hankali kan rawar da manema labarai za su taka wajen yaƙi da matsalar ƙarancin jini a jiki, ya tattauna illolin da matsalar ke haifarwa ga…
Rahotanni sun bayyana cewa, zuwa yanzu Kwamishinoni 5 tare da jami’an Gwamnatin Jihar Kano 10, ne su ka ajiye muƙamansu tare da jaddada biyayya da goyon baya ga jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka raba gari tsakanin Kwankwaso, da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif. Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara Kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates ta tattaro wannan adadi ne daga abin da ya bayyana zuwa safiyar ranar Talata 27 ga Janairun 2026. Daga cikin kwamishinonin da su ka yi…
