Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Adana Tarihi Da Al’ada: Shugaban Hukumar Tarihi Na Kano, Arc. Ahmad Zai Karbi Kyautar Kasa Kwanan Nan
Kano

Adana Tarihi Da Al’ada: Shugaban Hukumar Tarihi Na Kano, Arc. Ahmad Zai Karbi Kyautar Kasa Kwanan Nan

February 4, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260204 WA0033

DAGA SALISU MAISAJE

 

Manajan Daraktan Hukumar Tarihi Da Al’adu Ta Jihar Kano, Arc. Ahmad Abba Yusuf na sahun gaba kan sunayen da a ke bincike a kan su dan ba da lambar girmamawa kan hobbasa wajen raya al’adu da kuma alkinta tarihin al’umma.

Hadaddiyar kungiyar kungiyoyin dake nazari kan tarihi da al’adu na yammacin Afirka, dake da ofis a jihar Edo, ta shirya tsaf dan bayyana sakamakon wadanda su ka yi fice kan kudurorin da a ka yi nazari a kansu a shekarar da ta wuce ta 2025, na irin wadannan hukumomi.

Najeriya: Fiye da rabin mata masu juna biyu na fama da ƙarancin jini, in ji Gwamnatin Tarayya 

Bayanan farko farko na nuni da cewa Manajan Daraktan na Kano ya na sahun gaba saboda la’akari da yadda yake kokari wajen ganin ya kara dawo da kima da muhimmancin hukumar cikin shekarar da ta gabata.

An gano cewar jihar Kano ta jima ba ta kula da muhimmancin hukumar a gwamnatocin baya. Amma daga zuwan gwamna Eng Abba Kabir Yusuf sai abubuwan su ka fara samun canji. Musamman yadda ya yi hangen nesan ba wa Arc. Ahmad shugabancin wajen.

A yadda labari ya same mu mun gano cewar, Arc Ahmad mutum ne wanda ke tafiyar da shugabancinsa bisa dattako duk da cewar ba yawan shekaru gare shi ba. Kuma ya kasance mai kishin cigaban jihar Kano ne tare da al’ummar ta.

Wannan yabon da zai samu, babban abu ne sa zai kara kusanta wasu hukumomin duniya da wasu gwamnatocin kasashen waje masu rajin fafutukar kara alkinta tarihi da al’adun mutanen dake doron wannan duniya ta mu.

Bayanan farko farko na wannan bincike da hadaddiyar kungiyar ta ke daf da kammalawa, sun nuni da cewar, a jihohin arewacin Najeriya, jihar Kano ce kadai ta ke cikin wadanda ke sahun gaba na cin wannan lambar yabo.

An kuma kara da cewa, shi shugaban hukumar tarihi da al’adun na jihar Kano, mutum ne wanda yake bin tsarin tafiyar da aikin gwamnati sau da kafa. Hakan ya kara tabbatar da gaskiyar sa da rikon amanar sa. 

Maisaje ya rubuto wannan ne daga Abuja

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamnan Kano ya sauke shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Abdullahi Musa daga mukaminsa

March 11, 2026

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

March 6, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

Shugaba Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

February 23, 2026

Rundunar ‘yan sandan Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomin birnin kano da Ungogo

February 21, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.