Wata ƙungiya mai zaman kanta ta bayyana damuwa kan yadda yawaitar kananan yara masu rayuwar titi ke ƙaruwa a Kano, inda ta ce adadinsu ya haura miliyan biyu. Ƙungiyar Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI) ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa dubban yara na kwana a tituna da wuraren jama’a a kowace rana, cikin yanayi mara tsafta da rashin tsaro. Gobara Ta Lalata Shaguna Sama Da 1,500 A Kasuwar Singer Dake Kano Babban Daraktan ƙungiyar, Mohammed Ali Mashi, ya shaida wa manema labarai cewa da dama daga cikin yaran ana aiko su ne daga ƙauyuka…
Author: Wafsym
Jiragen saman sojin Amurka sun fara sauka a birnin Maiduguri na jihar Borno, lamarin da ke nuni da fara wani sabon tsarin haɗin gwiwa na tsaro tsakanin Amurka da Najeriya. Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa wani jirgin sojin Amurka ya sauka da daren Alhamis a filin jirgin saman birnin da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar. KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan Bayanai sun kuma nuna cewa ana sa ran sake saukar ƙarin wasu jiragen a ƙarshen mako a wani ɓangare na shirin aikewa da kusan dakarun sojin Amurka…
Wata babbar gobara da ta tashi a Kasuwar Singer da ke birnin Kano ta lalata shaguna da kwantena sama da 1,500, tare da haddasa asarar dukiyoyi da aka kiyasta sun haura Naira biliyan 5. Shugaban ƙungiyar ci gaban kasuwar, Junaid Zakari, ya bayyana cewa yankin da gobarar ta fi kamawa na ɗaya daga cikin wuraren kasuwar da suka fi cunkoso da kayayyaki masu daraja. NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano Da yake zantawa da kafar labarai ta SolaceBase, ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar ta cinye rumfuna…
A daidai lokacin da ya rage ‘yan kwanaki kaɗan a shiga watan Ramadan mai alfarma, mazauna jihar Kano na fuskantar tashin gwauron zabi na farashin kayan masarufi, musamman waɗanda ake amfani da su wajen shirya buɗa baki. Wani bincike da Daily News 24 ta gudanar a wasu manyan kasuwannin Kano, ciki har da Sheka da Rimi, ya nuna cewa farashin kayayyaki irin su zobo, tsamiya da kayan ƙamshi ya ƙaru da kusan kashi 60 cikin ɗari cikin makonni biyu kacal. NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano Wasu ‘yan kasuwa…
Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ceto wasu mata bakwai da ake zargin ana shirin safarar su zuwa ƙasar Iraki, bayan samamen da jami’anta suka kai wani otel a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano. Hukumar ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar shiyyar Kano ta samu, lamarin da ya kai ga kuɓutar da matan masu shekaru tsakanin 21 zuwa 24. Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A kaduna Jami’in hulɗa da jama’a na NAPTIP a Kano, Mohammed Habib, ya ce jami’an hukumar sun kai farmakin ne a ranar Alhamis,…
Wata tirela ta murkushe mutum biyu har lahira a kan babban titin Nnamdi Azikiwe da ke cikin garin Kaduna a daren Talata. Shaidun gani da ido sun ce mutanen da abin ya rutsa da su, namiji da mace, suna kan babur ne lokacin da tirelar ta kwace ta taka su, inda suka mutu nan take wajen misalin karfe 9:00 na dare. Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf A Matsayin Shugaban NAHCON Wani shaidan da ya zanta da Wakila Jaridar AMINIYA ya ce lamarin ya tayar masa da hankali, inda ya ce, “Gaskiya abin babu dadi. Namijin da macen…
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), inda ya nemi Majalisar Dattawa ta gaggauta tabbatar da naɗin. Naɗin ya yi daidai da tanadin sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta shekarar 2006, kamar yadda wasiƙar da shugaban ƙasar ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ta bayyana. Dalilin Da Ya Sa Na Ajiye Shugabancin NAHCON – Abdullahi Saleh Pakistan Rahotanni sun nuna cewa naɗin Ambasada Yusuf ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ya yi a…
Wani sabon bincike da hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta fitar ya nuna cewa mata a Najeriya sun fi maza nesa ba kusa ba wajen yin aikin tiƙi da kula da iyali ba tare da biyansu ba. Rahoton ya ce mata na shafe kusan kashi 21 cikin 100 na ranarsu, wato kusan sa’o’i biyar, suna yin irin waɗannan ayyuka, yayin da maza kuma kashi 4.1 cikin 100 ne kacal, kusan awa daya kenan suka shafewa. Dalilin Da Ya Sa Na Ajiye Shugabancin NAHCON – Abdullahi Saleh Pakistan Binciken, shi ne karon farko da aka gudanar da cikakken bincike a matakin…
Tsohon shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana dalilansa na ajiye aiki. Cikin sanarwarsa ta ajiye aiki da aka wallafa a shafin NAHCON, Farfesa Pakistan ya ce ya ajiye aikin en bisa dalilansa na raɗin kai. A ranar Litinin da maraice ne bayanai suka fara fitowa game da ajiye aikin Pakistan. Jihar Abia Ta Sanya Hannu Kan Dokar Tallafin Tsofaffi Cikin wasiƙar ajiye aikin nasa, Farfesa Pakista ya ce ya aike wa Shugaba Tinubu wasiƙa tare da sanar da shi matakin da ya ɗauka na ajiye aiki. Farfesa ya gode wa shugaban ƙasar bisa ”alfarmar” da…
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya sanya hannu kan Dokar Kula da Tsoffi wadda ke ba da gata na musamman ga duk ɗan asalin jihar da ya kai shekara 60 zuwa sama. Sabuwar dokar ta tanadi: Albashi na wata-wata kyauta Jinya kyauta a asibitoci Sauran alawus-alawus da tallafi har zuwa rasuwa Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nuna Alhini Kan Rasuwar Mutane 30 A Hatsarin Mota A Gezawa An ce manufar dokar ita ce rage raɗaɗin rayuwa ga tsofaffi, da tabbatar da walwalarsu, da kuma basu kariya ta zamantakewa bayan ritaya ko rashin ƙarfi. Masu sharhi na ganin matakin zai iya…
