Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Fiye da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO
Afrika

Fiye da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO

February 16, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
images~2

‎Wata ƙungiya mai zaman kanta ta bayyana damuwa kan yadda yawaitar kananan yara masu rayuwar titi ke ƙaruwa a Kano, inda ta ce adadinsu ya haura miliyan biyu.

‎Ƙungiyar Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI) ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa dubban yara na kwana a tituna da wuraren jama’a a kowace rana, cikin yanayi mara tsafta da rashin tsaro.

‎Gobara Ta Lalata Shaguna Sama Da 1,500 A Kasuwar Singer Dake Kano 

‎Babban Daraktan ƙungiyar, Mohammed Ali Mashi, ya shaida wa manema labarai cewa da dama daga cikin yaran ana aiko su ne daga ƙauyuka ko jihohin maƙwabta domin neman ilimin addini, amma sakamakon yunwa da rashin kulawa suna barin karatu su rungumi rayuwar titi.

‎Ya ce irin wannan rayuwa na jefa yara cikin haɗarin cin zarafi, aikata laifi da kuma rikici da doka, yana mai gargadin cewa matsalar na iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.

‎Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati, shugabannin al’umma da malamai su haɗa kai domin samar da mafita, ciki har da matsuguni, ilimi, abinci da kulawar lafiya ga yaran.

‎Haka kuma ta jaddada buƙatar rage talauci a karkara da wayar da kan iyaye kan muhimmancin kulawa da ‘ya’yansu, tana mai cewa dole ne neman ilimi ya tafi tare da kare lafiyar da jin daɗin yara.

‎GIOPPINI ta yi gargadin cewa rashin ɗaukar mataki cikin gaggawa na iya haifar da ƙarin matsalolin zamantakewa da na tsaro a nan gaba.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatu Mai Dauke Da JSS Da SS A Makarantun Sikandire A Najeriya

June 30, 2026

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎

June 30, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.