Author: Wafsym

Wasu jam’iyyun siyasa na adawa a Nijeriya sun yi watsi da Dokar Zabe ta 2026 da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ita kuma Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu, inda suka bukaci a fara sabon gyara cikin gaggawa kan abin da suka kira “tanade-tanade masu tauye dimokuradiyya” a cikin dokar. A wani taron manema labarai mai taken “Kiran Gaggawa Don Ceto Dimokuradiyyar Nijeriya” da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, shugabannin adawar sun ce dokar a yadda take yanzu na iya raunana gaskiya da sahihancin zabe tare da rage amincewar jama’a da tsarin kada kuri’a. Yayin…

Read More

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Asabar, 16 ga Janairun 2027, a matsayin ranar gudanar da Zaɓen Shugaban Ƙasa da Majalisar Tarayya. Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja. Ya ƙara da cewa, za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2027. INEC ta ce ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun maita ga ƙorafin da wasu ke yi game da jaddawalin…

Read More

Tun bayan naɗin sabon Sufeto Janar na ’yan sanda a Nijeriya wasu masana tsaro suka fara sharhi kan dimbin kalubalen da ke gabansa, musamman idan aka yi la’akari da tarin matsalolin tsaron da kasar take fama da su a halin yanzu. Olatunji Rilwan Disu ya maye gurbin Kayode Egbetokun ne wanda ya yi murabus ranar Talata. A watan Yunin 2023 ne Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya naɗa Kayode Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na ‘yansandan An haifi sabon mukaddashin ’yan sandan ne a jihar Legas da ke kudu masu yammacin Nijeriya ranar 13 ga watan Afrilun 1966. Ya shiga aikin…

Read More

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun danka matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Danmodi a daren Jiya a hedikwatar Hukumar dake Abuja. Gwamnan ya samu rakiyar Shugaban majalisar dokokin Jihar da Kwamishinan shari’a da Kwamishiniyar lamuran mata. Ana sa ran Gwamnatin jihar zata Kula da Walidan. Kwastam Ta Kama Miyagun Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 99.9, Ta Miƙa Su Ga NDLEA A Sakkwato In ba a manta ba dai takaddama ta dabaibaye batun matashiyar mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare…

Read More

Hukumar Kwastam ta Ƙasa a yankin Sakkwato da Zamfara ta kama miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira miliyan 99.9, sannan ta miƙa su ga Hukumar NDLEA a Sakkwato. Kwanturulan yankin, Aliyu Musa Ndako ne, ya miƙa ƙwayoyin ga kwamandan rundunar NDLEA na jihar. Dakarun Soji Sun Daƙile Harin Lakurawa Kan Wata Kasuwa a Kebbi Ndako ya ce jami’an Kwastam sun cafke kayayyakin ne bayan wani da ba a san ko wane ne bar su a ƙauyen Maidoro da ke kan titin Sakkwato zuwa Illela. Ya ce miyagun ƙwayoyin sun haɗa da kwalaye 182 na maganin tari na CST mai…

Read More

Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Riley Moore, sun miƙa wa Fadar White House wani rahoto na musamman kan zargin tsananta wa Kiristoci a Najeriya, inda suka jaddada buƙatar a sanyawa ƙasar takunkumi. Rahoton ya ba da shawarar sanyawa da kuma jaddada takunkumin hana biza ga duk mutumin da aka samu da hannu wajen tauye hakkin addini ko kisan Kiristoci a Najeriya. Dakarun Soji Sun Daƙile Harin Lakurawa Kan Wata Kasuwa a Kebbi Wannan rahoto ya biyo bayan bincike ne da Shugaba Trump ya umarci Riley Moore da Tom Cole su jagoranta, inda suka bayyana Najeriya a…

Read More

Dakarun Sojin Najeriya da ke cikin runduna ta musamman mai yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso yammacin ƙasar wato Fansar Yamma sun sanar da nasarar kashe tarin ƴan ta’addan Lakurawa a jihar Kebbi a dai dai lokacin da ƴan ta’addan suka nufaci kai wani hari a jihar Kebbi. Masanin tsaron yankin tafkin Chadi Zagazola Makama da ke sanar da wannan nasara ta dakarun Sojin Najeriyar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce tun da farko ƴan ta’addan suka ɗauki azamar kai hari wata kasuwar ƙauye ce a safiyar jiya Lahadi da ke garin…

Read More

Wani lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama a Najeriya, Barista Hamza Nuhu Dantani ya rubuta wata wasiƙa zuwa ga Hukumar tsaron farin kaya DSS ta ƙasar, inda yake nuna damuwa dangane da yadda ya ce hukumar ta ɗauki batun zargin sacewa, da kuma yin lalata da wata mace, Walida Abdulhadi, da ake zargin ɗaya daga cikin jami’anta Ifeanyi Onyewuenyi da yi. A cikin wasiƙar, lauyan ya saka ayar tambayar kan dalilan ƙin miƙa yarinyar ga iyayenta da kuma abin da ya kira ƙoƙarin kare jami’in da hukumar ke yi. Ƴan Bindiga sun sa harajin miliyan 100 ga malaman da ke…

Read More

A wani yanayi da matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya, ƴanbindiga sun buƙaci malamai su biya harajin naira miliyan 100 gabanin samun damar yin wa’azi a wani yanki na jihar Kebbi. Al’umma sun shiga tashin hankali a garin Utouno na ƙaramar hukumar Ngaski da ke jihar ta Kebbi guda cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaron, bayan samun umarnin biyan wannan kuɗi gabanin gudanar da wa’azi ko kuma Tafsiri cikin watan da muke na azumin Ramadana. Shugaba Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers Wasu…

Read More

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya murna da waɗanda suka yi nasara a zaɓukan Abuja da jihohin Kano da Rivers. A ranar Asabar ne INEC ta jagoranci gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomin Abuja, babban birnin ƙasar da na cike gurbi a jihohin Kano da Rivers. Shugaba Tinubu ya buƙaci waɗanda suka yi nasara a zaɓukan su nuna kishin ƙasa da sadaukarwa, sannna su auki nauyin da al’umma suka ɗora musu da muhimmanci ta hanyar riƙon amana da aiki da gaskiya.. Jam’iyyar APC ce ta lashe ƙananan hukumomi biyar cikin shida na Abuja, yayin da PDP ta samu ɗaya. Shugaban…

Read More