Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, reshen Kano, ta kai samame a wurare da dama da ake sayar da miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano, inda ta kama mutane akalla 56, ciki har da wani da ake zargi da hannu a kisan kai da aka yi shekaru biyar da suka gabata. A cewar hukumar, an samu nasarar kama mutanen ne bayan wani samame na kwanaki uku a jere, wanda aka gudanar mai taken “Operation Ramadan Mubarak” da ake ci gaba da yi. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya tabbatar da kama waɗanda…
Author: Wafsym
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abdullahi Musa, daga mukaminsa nan take. Haan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar. Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na sake farfado da tsarin aikin gwamnati domin inganta kwarewa, ladabi da kuma kyakkyawan gudanar da ayyuka a hukumomin gwamnati. Gwamnan ya gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar bisa gudunmawar da ya bayar wajen hidimtawa jihar Kano tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba. Hakazalika, an umarci Bilkisu…
Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ba shakka sun tayar da gagarumin rikici na siyasa, kace-nace tare da kara zurfafa rashin jituwa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon jagoransa na siyasa, Dr Rabiu Musa Kwankwaso. An tabbatar da cewa akalla ‘yan majalisa 38 ne suka rattaba hannu kan takardar neman tsige mataimakin gwamnan bisa zargin aikata manyan laifuka, amfani da mukami ba bisa ka’ida ba da kuma karya amana ta jama’a. Takardar da aka gabatar a zaman majalisar ta ce tana bin tsarin Sashe na 188…
Ma’aikatar tsaron ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce mambobi biyu na rundunar sojin ƙasar sun mutu bayan da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari sakamakon tangarɗar na’ura. Har yanzu ba a tabbatar ko lamarin yana da alaƙa da rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran ba. RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki Ma’aikatar tsaron ta ce mutanen biyu da suka mutu suna “cikin aiwatar da aikin ƙasa ne” a lokacin da hatsarin ya faru ranar Litinin. Ta kuma bayyana cewa…
Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin tsaro a matakin al’umma, ta fara samun tasiri duk da cewa ba ta jima da fara aiki ba. Rundunar ta fara aiki a hukumance a ranar 23 ga Disamba, 2025, kuma a cikin watanni uku da suka gabata, jami’anta sun fara taka rawa a fannoni kamar tattara bayanan sirri, dakile yunƙurin garkuwa da mutane, kai ɗauki lokacin gobara da kuma taimakawa wajen gano masu aikata laifuka. Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya Sai dai duk da wannan ci gaba,…
An nada dan marigayi Ayatullah Ali Khamenei a wannan mukami ne yayin da ake dab da cika kwanaki 10 da barkewar yaki a tsakanin Iran da Amurka da Isra‘ila wanda ya tsayar da harkoki a yankin Gabas ta Tsakiya. Majalisar manyan malaman Iran ce ta sanar da cewa Mojtaba Khamenei ne zai gaji mahaifinsa a matsayin babban jagoran ƙasar. An sanar da naɗin Mojtaba Khamenei mai shekara 56 a ranar Lahadi, bayan ƙuri’ar da majalisar malaman addini ta ƙasar ta kaɗa domin zaɓar wanda zai gaji mahaifinsa. An haifi Mojtaba Khamenei a ranar 8 ga watan Satumba na shekarar 1969…
Daga wannan Lahadi farashin man fetur a birnin Legas na Najeriya ya yi tashin gwauron zabi, inda yanzu ya kai tsakanin ₦1,040 zuwa ₦1,080 a kowace lita a gidajen mai daban-daban. Wannan ƙarin ya biyo bayan hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, sakamakon faɗaɗa yaƙi tsakanin kasashen Amurka, Isra’ila, da kuma Iran wanda ke barazana ga harkar man fetur. Tashin hankali a yankin Gabas Ta Tsakiya, wanda ya haɗa da hare-hare kan jagororin Iran da cibiyoyin man fetur, ya sanya farashin ɗanyen mai na Brent ya kusanci dala $90 zuwa $100 a kowace ganga. Wannan lamari ya jefa kasuwannin…
Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar Alhamis ta ƙaddamar da matakan tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin aikata ba daidai ba, amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba da kuma cin amanar ƙasa. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala ne ya gabatar da takardar sanarwar tsigewar a zauren majalisar, inda ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne daidai da sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara). Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran –…
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana bukatar a saka Amurka cikin tsarin zaben sabon shugaban Iran. Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta Axios ranar Alhamis, kwanaki biyar bayan kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a wani hari da Amurka da Isra’ila suka kai kan gidansa a Tehran. Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna A cewar Trump, Iran na bata lokacinta idan ta yi kokarin nada sabon jagora ba tare da sa hannun Amurka ba. Ya kuma bayyana cewa Mojtaba Khamenei, ɗan marigayi Ali Khamenei…
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, kwamared Aminu Abdulsalam, bisa zarge-zargen aikata manyan laifuka a kan aiki, wulaƙanta aiki da kuma karya dokokin aikin gwamnati. Matakin ya biyo bayan wani ƙorafi da ɓangaren zartarwa ya gabatar wa majalisar, inda aka buƙaci ta ɗauki mataki a kan Abdulsalam kan wasu zarge-zargen da suka shafi yadda ya gudanar da aikinsa a lokacin da yake kwamishinan ƙananan hukumomi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024. Gwamnatin Jigawa Ta Tsige Alƙalin Kotun Musulunci Kan Rashawa Da yake karanta ƙorafin, Shugaban nasu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce sanarwar ta…
